Al’ummar Arewa mazauna Kudu sun kulla yarjejeniya da PDP

Al’ummar Arewa mazauna Jihar Kuros Riba sun mika bukatunsu ga gwamnatin jihar, bayan sun yi yarjejeniya a tsakaninsu, cewa matukar suka zabi jamiyyar PDP, za ta cika musu muradun nasu da suka mika mata. Hakan ya biyo bayan wata ganawa ta keke da keke da aka yi tsakanin Gwamnan jihar, Liyel Imoke da makarraban yakin […]

Al’ummar Arewa mazauna Kudu sun kulla yarjejeniya da PDP
Al’ummar Arewa mazauna Kudu sun kulla yarjejeniya da PDP

Al’ummar Arewa mazauna Jihar Kuros Riba sun mika bukatunsu ga gwamnatin jihar, bayan sun yi yarjejeniya a tsakaninsu, cewa matukar suka zabi jamiyyar PDP, za ta cika musu muradun nasu da suka mika mata.

Hakan ya biyo bayan wata ganawa ta keke da keke da aka yi tsakanin Gwamnan jihar, Liyel Imoke da makarraban yakin neman zaben a harabar hedkwatar karamar Hukumar birnin Kalaba da yammacin Talatar da ta gabata.
Mutanen da suka gabatar da jawabi wajen ganawar kuma suka mika bukatun nasu ga gwamnatin sun hada da Barista Musa Maigoro daga Ikom, wanda ya nemi gwamnati da ta daina samun nasarar yaki tana barin ’yan Arewa da kuturun bawa. Ya bayyana cewa tunda a siyasance ’yan Arewa na bin su sau da kafa kuma ana zaune lami lafiya tare da mutunta juna tsakani, yau shekara sama da dari, don haka “muna bukatar idan an kafa gwamnati a sanya ’yan Arewa a cikin mukarraban gwamnati kamar yadda Gwamnan Jihar Kano; Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi, ya dauki kabilar Kudu maso gabas da na Kudu maso yamma da ma na yankin Neja Delta ya ba su mukamai a gwamnatinsa. Sannan akwai ’yan Arewa da suka kammala karatu a manyan kwalejoji da kuma jami’a a jihar, a rika daukar su aiki.”
Ya ci gaba da cewa tun daga shekara ta 1999 zuwa bana ’yan Arewa ke mara wa jam’iyyar PDP baya za kuma su ci gaba da yin hakan iyakar rai iyakar fama.
Shi kuwa shugaban matasan jam’iyyar PDP, Alhaji Ado Inuwa, lokacin da ya mike yake nasa jawabin, bukatu muhimmai ya gabatar wa gwamnatin da yake so ta cika musu, “farko a kafa musu cibiyar ’yan sanda a Layin Bagobiri; wato unguwar Hausawa; sakamakon fashi da makami da aka yi a unguwar kwanan baya, sannan kuma a kafa musu hukumar alhazai domin magance takaddama da ake samu kowace shekara wajen rabawa da kuma bayar da kujerun aikin Hajji da gwamnatin jiha ke yi, musamman zamanin Gwamna Imoke.” Haka kuma bukataun na ’yan Arewar sun kara da samar wa unguwar Nasarawa tiransifoma.
Da yake mayar da jawabi nan take, Gwamna Liyel Imoke cewa ya yi: “Za mu cika muku muradunku amma fa zaben da za a yi, ku tabbata kwai da kwarkwata maza da mata kun tafi wajen jefa kuri’a kun zabi jam’iyyar PDP. Za mu biya muku dukkan bukatunku, musammman ma idan sabon gwamna ya hau mulki.”
Da ya juya kan batun hukumar alhazai da bayar da tiransifoma, nan take gwamnan ya ce a mika masa sunan wanda suke so a nada, na’urar tara wutar lantarki kuma ya yi alkawarin za a kai musu guda biyu.
Dangane da batun nada ’yan Arewa a mukarraban gwamnati, gwamnan ya umurci Farfesa Ibara Esu, mataimakin dan takarar gwamna Ben Ayade, ya tabbata da zarar sun kafa gwamnati an yi hakan.
Bukatu ne da daman gaske ’yan Arewar suka gabatar amma bisa yarjejeniyar sai sun zabi jam’iyyar PDP kafin su gani a kasa. Wani tsokaci da ya yi cikin jawabin, gwamnan ya ce shi baya goyon bayan a yi takardar shaidar zama dan yanki, “ina laifi a ce mutum ya yi satifiket na zaman wuri kamar yadda ake yi a Amurka, misali yadda dan asalin Washington da ke zaune a Alabama yake yin satifiket na zaman wurin.