Al’ummar Attat sun nemi a tsige hakiminsu kan karkatar da taki

Al’ummar Attat da ke karamar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna sun nemi a tsige hakiminsu Mista Casmia Zamani Ango bisa samunsa da laifin karkatar da takin zamani da aka ce a rabar wa mutanen yankin da kotu ta yi.Da yake jawabi a madadin al’ummar yankin shugaban kungiyar Ci-gaban Attat, Mista Patrick Tanko wanda ya […]

Al’ummar Attat sun nemi a tsige hakiminsu kan karkatar da taki

Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan YeroAl’ummar Attat da ke karamar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna sun nemi a tsige hakiminsu Mista Casmia Zamani Ango bisa samunsa da laifin karkatar da takin zamani da aka ce a rabar wa mutanen yankin da kotu ta yi.
Da yake jawabi a madadin al’ummar yankin shugaban kungiyar Ci-gaban Attat, Mista Patrick Tanko wanda ya zanta da manema labarai a Kaduna, ya nuna bakin cikinsa game da yadda Hakimin ya ki sauka daga mukaminsa duk da samunsa da laifi da kotu ta yi.
A cewarsa, al’ummar yankin sun dandana kudarsu saboda rashin ingancin amfanin gona a bara sakamakon karkatar da takin da Mista Casmia ya yi.
“Mun shiga halin ha’ula’i sakamakon karkatar mana da taki da aka yi wanda hakan ya sa muke yin kira gare shi ya sauka daga mukaminsa saboda wannan laifi da ya aikata mana. Wannan shi ne abin da mutanenmu ke so bayan mun zauna taro da su. Muna kuma yin kira ga gwamnatin jihar ta shigo cikin zancen domin ceto yankinmu daga mulkin kama-karya,” inji shi.  
A cewarsa, a ranar 30/4/2013 ne wata Kotu a Kafanchan ta yanke wa Mista Casmia Zamani Ango da Marshal Jacob, wani tsóhon kansilan yankin da ke wakiltar mazabar Madakiya wanda ya hada da yankin Attat, hukuncin zaman kaso na wata uku ko biyan tarar Naira dubu 100, saboda samunsu da laifin karkatar da takin.
Ya nuna wa manema labarai kwafin hukuncin da kotun ta yanke wa wadanda ake zargi a lokacin. Kuma kotun ta ce ta yi musu sassauci ne saboda rokon da lauyansu ya yi cewa wannan ne karon farko da suka aikata irin wannan laifi.
Da aka tuntubi hakimin ta waya ya ki cewa komai dangane da kiran da aka yi na a cire shi daga mulki. Game da hukuncin da kotu ta yanke masa na karkatar da taki kuwa, sai ya ce yana da ja. Ya ce kuma zai daukaka kara domin neman ’yancinsa.