Al’ummar Bare-bari sun kafa kungiya a Ghana

Masu iya magana na cewa kowa ya bar gida, gida ya bar shi. A dalilin wannan karin magana ne al’ummar Kanuri (Bare-bari) a Ghana a bisa shugabanci Babban Limamin kasar Shiekh Dokta Osman Nuhu Sharubutu suka kafa kungiyan Bare-bari wace aka kaddamar ranar Asabar da ta gabata a gidan babban limamin da ke unguwar Fadama. […]

Al’ummar Bare-bari sun kafa kungiya a Ghana
Al’ummar Bare-bari sun kafa kungiya a Ghana

Masu iya magana na cewa kowa ya bar gida, gida ya bar shi. A dalilin wannan karin magana ne al’ummar Kanuri (Bare-bari) a Ghana a bisa shugabanci Babban Limamin kasar Shiekh Dokta Osman Nuhu Sharubutu suka kafa kungiyan Bare-bari wace aka kaddamar ranar Asabar da ta gabata a gidan babban limamin da ke unguwar Fadama.

A cikin jawabinsa Shiekh Dokta Osman ya bayyana cewar hadin kan alumar kasa baki daya ne burinsa. Kuma ya ce: “Na gode wa Allah kwalliya ta biya kudin sabulu saboda yau zamantakewa tsakanin kabilu da addinai daban-daban sai godiya domin babu wani bambanci. Kowa ya fahimci cewa kowa na da ’yancin yin ibadar da yake so muddin dai be wuce gona da iri ba.”
Bukin ya samu halartar mashahuran mutane ciki har da Babban Limamin Ahli Sunna wa Jama’a na kasa wato Shiekh Umar Ibrahim Imam da Babban Sarkin Bare-barin a Jihar Accra, Alhaji Yusif Zannua.
Bare-bari sun shigo kasar Ghana ne ta fuskoki daban- daban. Akwai wadanda fatauci ya kawo su da wadanda aure ne ya kawo su, sai kuma wadanda neman ilimi ya shigo da su daga kasashen Najeriya da Chadi da Kamaru da Laberiya da Nijar da sauransu.