Al’ummar Bauchi na ci gaba da jimamin rasuwar Falakin Katagum

 Kwamishinan Watsaa Labarai na Jihar Bauchi, Alhaji Umar Ibrahim Sade ya bayyana cewa Gwamnati da al’ummar Jihar Bauchi suna jimamin rasuwar Kwamishinan Ma’aikatar Raya Karkara na Jihar Bauchi, Injiniya Mahmood Abdullahi Abubakar, Falakin Katagum. Kwamishinan ya bayyana alhininsa ne a sakon ta’aziyyar da ya aika wa manema labarai a Bauchi. Ya ce “Duk mai rai […]

Al’ummar Bauchi na ci gaba da jimamin rasuwar Falakin Katagum
Al’ummar Bauchi na ci gaba da jimamin rasuwar Falakin Katagum

 Kwamishinan Watsaa Labarai na Jihar Bauchi, Alhaji Umar Ibrahim Sade ya bayyana cewa Gwamnati da al’ummar Jihar Bauchi suna jimamin rasuwar Kwamishinan Ma’aikatar Raya Karkara na Jihar Bauchi, Injiniya Mahmood Abdullahi Abubakar, Falakin Katagum.

Kwamishinan ya bayyana alhininsa ne a sakon ta’aziyyar da ya aika wa manema labarai a Bauchi. Ya ce “Duk mai rai mamaci ne, kowa kuma da lokacins, Falaki lafiyarsa kalau, ya dawo gida ne ya yi hutun karshen mako da iyalansa da ’yan uwansa a Azare sai kawai ya samu gajeruwar rashin lafiya, kuma Allah Ya karbi rayuwarsa.”

“Kuma saboda yadda yake jan jama’a a jika, suke kaunarsa, jim kadan da ba da sanarwar rasuwarsa sai jama’a suka yi ta turuwa zuwa garin Azare, ciki har da Gwamnan Jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar, aka yi masa Sallah, aka kai shi kushewarsa,” inji shi.

Alhaji Sade ya ce Falaki mutumin kirki ne, jajirceccen dan siyasa mai hangen nesa da son zumunci da sakin fuska ga kowa. “Mu a Majalisar Zartarwar Jihar Bauchi, mun yi rashin abokin aiki, haziki, jajirtacce mai tunani da hangen nesa da kaifin hankali. Ba za mu mance irin gudunmawar da yake bayarwa ba wajen gina jihar nan da al’ummarta,” inji shi.

Sai ya kara da cewa Falakin Katagum mutum ne mai kaunar jama’arsa, wanda a kullum yana tare da mafi yawan abin da al’ummarsa suke so; ga shi karimi mai taimako ga al’ummarsa.

Kwamishinan ya roki Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa, Ya kuma isar da ta’aziyyarsa ga Gwamnan Jihar Bauchi da Mai martaba Sarkin Katagum da daukacin jama’ar jihar baki daya kan wannan babban rashi da aka yi.

An haifi marigayi Injiniya Muhammad Mahmood Abdullahi Abubakar ranar 16 ga watan Maris 1965 a garin Azare da ke Jihar Bauchi. Ya yi makarantar firamare a Gyallesu da ke Zariya daga 1971 zuwa 1977. Ya halarci Kwalejin Alhudahuda da ke Zariya daga 1977 zuwa 1982. Ya halarci Kwalejin Kimiyya da kere-kere da ke Kaduna, inda ya karanta ilimin taswirar gine-gine.  Ya kuma yi Diploma kan harkar Injiniya, duk a 1988. Ya kuma samu takardar shaidar Babbar Diploma kan aikin Injiniya a 1992, sannan ya kuma yi karatun digiri na biyu a Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi a 2013.

Marigayin kuma mamba nea  kungiyar Injiniyoyi ta kasa. Ya fara aiki ne a Kwalejin Ilimi ta Aminu Saleh da ke Azare. Kuma ya yi ayyuka da dama har ya kai mukamin Darktan Kula da Sashen Ayyuka na Kwalejin. Kuma saboda kwazonsa ne aka nada shi Sarautar Falakin Katagum daga bisani kuma aka nada shi Kwamishinan Ma’aikatar Raya Karkara ta Jihar Bauchi. Ya rasu ya bar matan aure uku da ’ya’ya da dama.