… Al’ummar Damaturu na fuskantar tsadar rayuwa

Kwararowar ’yan gudun hijira daga wasu garuruwan Jihar Borno da rikicin Boko Haram ke addaba al’ummar garin Damaturu a Jihar Yobe na fsukantar tsadar rayuwa, inda suka fara ji a jikinsu, sakamakon tsawwalar farashin kayan masarufi da tsadar gidajen haya.Sannan al’ummar garin na kuma zaman dar-dar gudun kada batagari su boye a cikinsu a karshe […]

… Al’ummar Damaturu na fuskantar tsadar rayuwa
… Al’ummar Damaturu na fuskantar tsadar rayuwa

Kwararowar ’yan gudun hijira daga wasu garuruwan Jihar Borno da rikicin Boko Haram ke addaba al’ummar garin Damaturu a Jihar Yobe na fsukantar tsadar rayuwa, inda suka fara ji a jikinsu, sakamakon tsawwalar farashin kayan masarufi da tsadar gidajen haya.
Sannan al’ummar garin na kuma zaman dar-dar gudun kada batagari su boye a cikinsu a karshe su iya zama musu barazana.
Aminiya ta gano cewa adadin ’yan gudin hijirar da ke shigowa Damaturu na karuwa a kullum ta yadda kusan kowace sa’a za a tarar da mota dauke da jama’a na zuwa wasu na zuwa gidajen ’yan uwansu, yayin da wasu ke neman gidajen haya.
Wani magidanci da ya yi hijira daga Bama tare da matansa uku da ’ya’yansa 12 da ya nemi a sakaya sunansa kuma ya shaida wa Aminiya a tashar motar ta Damaturu cewa ya zo garin ne ba tare da ya san wurin da zai shiga ba. “Ban san kowa a garin nan ba, zan shiga gari ne neman gidan haya don samun yadda zan zauna da iyalaina na wani lokaci kafin na natsu ta yadda zan koma Bama in jami’an tsaro suka ceto garin namu,” inji shi.
Malam Saleh Bakwaro da ke unguwar Sabon Fegi a Damaturu ya shaida wa Aminiya cewa, in aka yi la’akari da yadda ’yan gudin hijirar ke tudadowa zuwa Damaturu akwai masu tsoron kada batagari su yi amfani da wannan dama su kawo nakasu ga zaman lafiyar da aka samu. Ya bukaci jami’an tsaro da masu unguwanni su sa ido ga masu shigowa don yi wa tufkar hanci.
Kuma ya nemi jama’ar gari su taimaka wajen sa ido ga duk bakon da ya shigo neman haya, kuma su taimaka wa baki na gaskiya da ke shigowa, saboda wanda ya jikan wani Allah zai jikansa.

An fara sana’ar hayar Fawa-bank a Kano

’Yan sanda sun kama fasinja ya ɓoye bindiga a cikin burodi 

An kama fasto kan kashe ’yar shekara 13 da duka

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya