Al’ummar Fulani a jihohin yamma sun yi taron neman mafita
Shugabannin kungiyar makiyaya ta Jamnati Fulbe a sashen kudu maso yammacin kasa sun yi wani taro a ranar Asabar a garin Abeokuta domin tattaunawa a kan irin gudunmawar da za su bayar ga sabuwar gwamnatin kasa domin dorewar mulkin dimkradiya a Najeriya. Kuma sun tattauna a kan yadda za a shawo kan matsalolin zamantakewa a […]
Shugabannin kungiyar makiyaya ta Jamnati Fulbe a sashen kudu maso yammacin kasa sun yi wani taro a ranar Asabar a garin Abeokuta domin tattaunawa a kan irin gudunmawar da za su bayar ga sabuwar gwamnatin kasa domin dorewar mulkin dimkradiya a Najeriya. Kuma sun tattauna a kan yadda za a shawo kan matsalolin zamantakewa a tsakaninsu da manoma da batun tsaron kasa.
Da yake yi wa ’yan jarida bayanin sakamakon taron na yini daya, Shugaban kungiyar Jamnati Fulbe reshen Jihar Ogun, Alhaji Abubakar Ibrahim Dende, ya ce: “Mun yi taron ne domin duba irin rawar da al’ummar Fulani makiyaya za su taka da irin goyon bayan da za mu bayar ga sabuwar zababbiyar gwamnatin kasarmu Najeriya wacce dan’uwanmu bafullatani Shugaba mai jiran gado Janara Muhammadu Buhari (mai ritaya) zai shugabance ta daga ranar 29 ga watan Mayu bayan an rantsar da shi. Matsalar tsaron kasa ce muka fi mayar da hankali wajen tattaunawa domin duba irin gudunmawar da za mu bayar, domin samar da zama lafiya da ci gaban kasa. Muna so sabuwar gwamnati ta kalli batun samar da filayen kiwo na dindindin ga makiyaya da satar shanu da idon rahama, musamman domin kasancewarmu ’yan kasar Najeriya da irin gudunmawar da muka dade muna bayarwa ga bunkasar tattalin arzikin kasa. Kamar yadda zababben Shugaba Muhammadu Buhari ya sha nanata cewa gwamnatinsa za ta dauki matakan murkushe ’yan Boko Haram da tsagerun Neja Delta. To kada ya manta da matsalar fadace-fadace tsakanin makiya da manoma da sace-sacen dabbobi bayan an kashe mana mutane. Wannan babbar matsala ce da ya dace a sanya ta cikin batun shawo kan matsalar tsaron kasa.”
“Wata babbar matsala da al’ummar Fulani mazauna Kudu maso yamma suke fuskanta, ita ce, irin yadda ake daukar mu a matsayin baki a cikin kasar haihuwarmu. Mahukunta da suka hada da kananan hukumomi da gwamnatocin jihohi 6 na wannan sashe ba su tafiya tare da mu duk kuwa da irin gudunmawar da muke bayarwa na bunkasar tattalin arzikinsu. Akwai manyan kasuwannin shanu fiye da 50 a cikin Jihar Ogun kadai, haka su ma sauran jihohi 5 na wannan sashe suke samar da dimbin kudaden shiga ga gwamnatocin wadannan jihohi amma an yi watsi da al’amuran da suka shafi mutanenmu.”
“Saboda haka muke so idan sabon shugaba Janar Muhammadu Buhari ya fara mulkin kasar nan, ya tuna da mu a nan Kudu maso yamma da muke fatan zai yi maganin irin wadannan matsaloli kamar yadda ya yi alkawari. Sau da yawa ana samun kuskure da dabbobinmu suke lalata amfanin gona da bai wuce a biya Naira dubu daya zuwa biyu ba amma sai a kama yaranmu a tsare kuma a tilasta mana biyan kudi Naira dubu 100 zuwa 200 bayan kudaden belin ’ya’yanmu. Wannan shi ne dalilin kafa wannan kungiya ta Jamnati Fulbe domin zama tare da manoma da muke tattauna yadda za a samo hanyar yin maganin wannan matsala domin samar da zama lafiya a tsakanimu da manoma, musamman da yake muna jin yaren juna. kungiyarmu ta dage wajen yin adalci a tsakanin makiyaya da manoma da muke tabbatar da hukumcin biyan diyyar kudin da ya dace ga manomin da aka lalata masa albarkar gonarsa. Saboda haka muke so mu ma a kalle mu a matsayin ’yan kasa, ba baki kamar yadda aka yi mana a wannan sashe ba.” Inji shi.