Al’ummar Gwamai na fuskantar barazanar zaizayar kasa

An yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da Majalisar karamar Hukumar Dawakin Tofa da kuma ma’aikatar kula da muhalli da su gaggauta daukar matakai na magance barazanar zaizayar kasa da ke neman lalata gidaje da gonaki a unguwar bayan makaranta Gwamai, yankin karamar Hukumar Dawakin Tofa. Wannan kira ya fito daga daya daga cikin mazauna […]

Al’ummar Gwamai na fuskantar barazanar zaizayar kasa

An yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da Majalisar karamar Hukumar Dawakin Tofa da kuma ma’aikatar kula da muhalli da su gaggauta daukar matakai na magance barazanar zaizayar kasa da ke neman lalata gidaje da gonaki a unguwar bayan makaranta Gwamai, yankin karamar Hukumar Dawakin Tofa.

Wannan kira ya fito daga daya daga cikin mazauna wannan unguwa da ke bayan makaranta Gwamai, Malam Auwalu Bala a madadin daukacin al’ummar garin na, inda ya bayyana cewa zaizayar kasar tana barazana ga muhalli da gonaki na mutanen bayan makaranta saboda zaftarewar da kasa ke yi a wannan bangare.

Sannan ya nuna cewa idan aka dauki mataki na dakile wannan zaizayar kasa, ko shakka babu an ceto muhallai da gonakin da ke kusa da inda abin ke faruwa, kana an yi abin da mutanen unguwar bayan makaranta ke bukata tun lokaci mai tsawo.

Ya ce suna so a samar da wata hanyar ruwa domin kauce wa wannan barazana ta zaizayewar kasa, sannan akwai bukatar wakilai daga Majalisar karamar Hukumar Dawakin Tofa da ma’aikatar kula da muhalli su ziyarci wannan guri domin ganin yadda unguwar ke fama da barazanar zaizayar kasa da yadda abin yake neman zamowa hadari ga al’ummar unguwar, musamman yara kanana idan an yi ruwa, tare da fatan cewa za su kai dauki, domin gyarawa.