Al’ummar Hausawa sun musanta labarin fada da sojoji a Legas

Hausawa masu kananan sana’o’i a yankin Ikorodu da ke Jihar Legas sun nisanta kansu da wata jita-jita da ake yadawa cewa sun yi rikici da sojoji a yankin nasu. Hausawan wadanda akasarinsu suke sayar da kayan marmari da kayan miya a bakin titin Ikorodu sun bayyana cewa ’yan gareji ne suka yi rikici da sojojin.Wani […]

Al’ummar Hausawa sun musanta labarin fada da sojoji a Legas
Al’ummar Hausawa sun musanta labarin fada da sojoji a Legas

Hausawa masu kananan sana’o’i a yankin Ikorodu da ke Jihar Legas sun nisanta kansu da wata jita-jita da ake yadawa cewa sun yi rikici da sojoji a yankin nasu.

Hausawan wadanda akasarinsu suke sayar da kayan marmari da kayan miya a bakin titin Ikorodu sun bayyana cewa ’yan gareji ne suka yi rikici da sojojin.
Wani mai suna Malam Usman ya ce: “Tun kafin sojojin su iso wurinmu tuni mun kwashe kayayyakinmu. Da suka zo wurin sai wasu ’yan gareji suka rika yi musu ihu, daga bisani sai sojojin suka rika dukan jama’a. Mu ba mu taba fada da wasu jami’an tsaro ba. Mu masu son zaman lafiya ne kuma mu masu bin doka da oda ne. Ai kai ma ka san labarin ba gaskiya ne ba, babu yadda za a ce Bahaushe ya dauki makami ya yi fada da mutanen gari ballantana sojoji. Kawai wani ne ya shirya labarin don ya bata mana suna.”
Malam Sulaiman Musa shi ma cewa ya yi: “Mu ma mun ji ana ta yada wannan magana amma mu mun san ba gaskiya ne ba. Ko su sojojin idan suka ji wannan magana za su karyata ta, don sun san ba yadda za a yi Bahaushen da ya zo neman abin da zai rufa wa kansa asiri ya yi fada da soja. Tunda muke yankin Ikorodu ba mu taba fada da wani jami’in tsaro ba.”
Shi kuwa Salisu Isa wani mai sayar da kayan miya kira ya yi ga jama’a da su rika yi musu adalci. “Ya kamata a rika yi mana adalci, ba a rika bata mana suna ba. Duk wata tarzoma da ta tashi sai a ce Hausawa ne suka yi. Mu mutane ne masu son zaman lafiya, arziki muke nema ba tsiya ba saboda haka babu yadda za a ce wani Bahaushe ya yi fada da soja.” Inji shi.
Sai dai duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Legas Kenneth Nwosu ya ci tura domin bai amsa wayar da aka buga masa ba kuma bai ba da amsar sakon wayar da aka tura masa ba.
Hakazalika su ma rundunar sojoji ta 9 da ke Jihar Legas ba su ce uffan ba dangane da lamarin.