Al’ummar Hausawan Accra sun nada sabon sarki
A kwanakin baya ne al’ummar Hausanawa da ke zaune a babban birnin kasar Ghana, Accra, suka yi wani gagarumin nadin sabon sarkinsu bayan rasuwar tsohon sarkin a watan Oktoban bara.An yi bikin nadin sabon Sarki, Alhaji Muhammad Kabir kadiri ne a filin taron Rawlings Park, wanda kuma ya samu halarta dimbin jama’a daga ciki da […]
A kwanakin baya ne al’ummar Hausanawa da ke zaune a babban birnin kasar Ghana, Accra, suka yi wani gagarumin nadin sabon sarkinsu bayan rasuwar tsohon sarkin a watan Oktoban bara.
An yi bikin nadin sabon Sarki, Alhaji Muhammad Kabir kadiri ne a filin taron Rawlings Park, wanda kuma ya samu halarta dimbin jama’a daga ciki da wajen birnin. A lokacin da ke jawabi, sabon sarkin ya bayyana farin cikinsa da Allah Ubangiji Ya nuna masa ranar da kuma godiya ga dubban jama’ar da suka halarci bikin.
Daga bisani kuma ya yi alkawarin yin aiki tukuru don tabbatar don wanzuwar zaman lafiya da fahimtar juna tsanin Hausawa da sauran kabilun kasar Ghana. Bayan nan ne kuma aka baje kolin kayayyakin al’adun Hausa.
Da wakilinmu ya tuntubi daya daga cikin mahalarta taron, Galadima Alhaji Usman kadir English kira ya yi ga gwamnatin Tarayyar Najeriya da su kara himma a kokarin da ake yi wajen ceto ’yan matan garin Chibok fiye da 200 da ’yan Boko Haram suka sace a cikin watan Afrilun bana. Ya ce, “kasancewa kasar Ghana da Tarayyar Najeriya kamar dan Juma ne da dan Jummai, duk wani abin da ya faru da daya ,sai ya yi tasiri ga gudar. Wannan ya sa muke rokon Ubangiji Allah ya yi maganin lamarin. Kuma muna fatan Allah Ya taya sabon Sarki riko”inji shi.