Al’ummar Jigawa a hau sikelin awon ci gaba
Editan Aminiya, ka ba ni dama in yi tsokaci kan yadda al’ummar Jihar Jigawa da Gwmanatinsu ke doki da murnar cikar jiharmu shekara 23 da kafuwa. Lallai Gwmanatin Jigawa da al’ummarta mu yi nazarin abubuwan da za su inganta rayuwarmu. Hakika abin farin ciki ne, domin ko budurwa ce, a wannan zamanin ana sa ran […]
Editan Aminiya, ka ba ni dama in yi tsokaci kan yadda al’ummar Jihar Jigawa da Gwmanatinsu ke doki da murnar cikar jiharmu shekara 23 da kafuwa. Lallai Gwmanatin Jigawa da al’ummarta mu yi nazarin abubuwan da za su inganta rayuwarmu. Hakika abin farin ciki ne, domin ko budurwa ce, a wannan zamanin ana sa ran an ilimantar da ita, boko da addini, har ta isa aure. Duk da haka muna son ganin gwamnanmu ya dora al’ummar jihar nan kan tafarkin ci gaba da kyawawan manufofinsa a tsawon shekarun da ya yi yana mulki. Lallai hakki ne da ya rataya ’yan asalin jihar Jigawa mu himmatu a kungiyance wajen taimaka wa ci gaban jiharmu. Inda kuma shugabanni suka yi kuskure, to mu ba su shawara, tare da fatan alheri, don samun ci gaba mai dorewa. Gumalawa da Hadejawa da sauran masarautun Jigawa, mazauna cikin gida da na waje, wjaibi ne mu kafa kungiyoyi tallafa wa ci gaban jiharmu a ko’ina muka samu kanmu. Mu daina fita ci-rani face mun san sana’ar da za mu yi, sannan mu himmatu wajen neman ilimi da dukiya, tare da koyon sana’o’I, da koyi da dabi’un mutanen kwarai. Allah Ya sa mu dace. Amin.
Addu’a ga kasa
Assalamu alaikum Aminiya mai farin jini, wanan hali da yan uwan mu na arewacin nageria ke ciki a halin yanzu abin akwai takaici da ban tausayi fatan mu a kulum shine Allah Ya ba mu zaman lafiya mai dorewa ameen Daga Umar Idirisa Askira jihar Borno 07034478412
Ga Gwamnati da jami’an tsaro
Gwamnatin Najeriya da jami’an tsaron kasar ba da gaske suke ba, a yakinsu da kungiyar Boko Haram , Sakacin Gwamnatin Tarayya na kara taimakawa rikicin cigaba . Watakila hakan ba zai rasa nasaba da zargin da ake yi wa gwamnatin ba, na maida jihohin Arewa tamkar ’yan’tawaye a Najeriya, ta yadda za a samu damar da za a yi amfani da ita, wajen wargaza kasar nan. Daga Mansoor Said Unguwar PRP Kano . 07039215954
Ga kungiyoyin Musulunci
Tabbas yunkurin da wasu kungiyoyin Musulmi a Kudu maso gabashin kasar na fahimtar da duniya cewa aikin addinin Musulunci na adawa da tashe-tashen hankula.ya yi daidai la’akkari da irin mummunar
aika-aikar da su masu tada kayar bayar suke ma mutanen da ba su ji ba su gani ba. Muna rokon Allah ya kawo muna zaman lafiya a Arewa da kowane lungu da sako na kasarmu Najeriya . Daga AbdulMalik Saidu Mai biredi, Tashar Bagu, Gusau. 08069807496.
Ina manyan Arewa?
Hakika Gwamnatin Najeriya ba ta mayar da hankalin kan rikicin Jihohin Borno da Yobe da Adamawa, to za a wayi gari wadannan jihohin sunkoma hannun ‘yan boko haram . Ana ta yi wa al’umma kisan kiyashi, duk da jami’an tsaron da aka jigbe a jihohin. Kuma babu wani babba mai fada aji a Arewacin Najeriya, wanda ya fito fili, ya nuna bacin ransa akan wannan cin zarafin da ake yi wa ‘yan Arewa. Daga.Ababakar Lawal Gidan danmaye a Jargaba Bakori , Jihar Katsina +2348097627776.
Ga Aminiya
An gaishe ku wakilan al’umma. Allah Ya kareku. Amin. Daga Sani Ya Mallam 08126466663.
Ga Sarkin Hadeja
Assalamu alaikum Edita. Don Allah ka ba ni ama in isar da sakona ga Mai martaba Sarkin Hadeja, Alhaji Adamu Abubakar Maje, Shugaban Majalisar Sarkunan Jihar Jigawa; Jagoran Talakawan Arewacin Najeriya. Allah Ya kara wa Sarki lafiya da zaman lafiya. Daga Yunusa Hamza (Gobenefa), Jihar Jigawa 08133183507
Laifin Jonathan
Tashin tashinar da ke aukuwa yankin Arewa maso Gabas laifin Shugaba Jonathan ne. Domin shi ne wanda alhakin tsaron rayukan al’umma ya rataya a kansa. Daga Adamu Aliyu Ngulde 09091513043.
Ga Garkuwan Shema
Edita don girman Alah ka ba ni fili in yi godiya, wurin Malam Gambo Rabi’u Bakori kan biyayya d ahadin kan da yake bai wa Gwamna Shema Mai albarka, wajen ci gaban Jihar Katsina. Mun gode amanar Baba Shema. Daga Amiru Isa Bakori 07068347933.
Ga Sarkin Zazzau Suleja
Edita ina neman dama domin ihn mika jinjinata ga Mai martaba Sarkin Zazzau Su8leja, Dokta Auwal Ibrahim CON FNAN, saboda tsayin dakansa wajen kare muradin al’ummarsa. Allah Ya kara wa Mai martaba lafiya, tare d anisan kwana. Daga dahiru Dauda (KGY) 08055552897.
Ga mahukuntan Najeriya
Abin da ’yan fashin Zamfara ke yi abin takaici ne. Ya kamata mahukuntan Najeriya su dauki mataki na dindin. Daga 08065946334.
Ga shuabanni APC
Amniniyar amana don Allah ga sakona ga shugabannin APC na Arewa maso Yamma, su sani mu magoya bayan Janar Buhari mun ja layi. Domin mu talakawa muna nan a APC don Buhari. In ba Buhari, babu APC. Daga Musa Unguwar Maiyasin, danja Jiahr Katsina 08155648155.
Dokar ta-baci illa ce
Assalamu alaikum. Edita da fatan za ka ba ni fili in yi tuni ga Shugaban ksa da majalisar kasa, wallahi an yi kuskuren sanya dokar ta-baci a jihohin Barno da Yobe da Adamawa, domin dokar ce ma ta kara tabarbarar da harkokin tsaro.Daga Ahmadu Bello dambatta CBDA. 08059439901.
Fadar Bege da Inyas a Gombe?
Assalamu alaikum, Aminiya ga sako nan ga ’yan Najeriya game da fitowar Fadar Bege das Inyas na halarci kauyen Kodon Kamaldeeba, Jihar Gombe. Na shiga gidan na samu yara da manya da matan aure, na kutsa kai, amma ban ga komai ba. Wai yaushe jama’a za su gane gaskiya? Daga Manu KC Gombe 07085285692.
Haba Shugaba Jonathan!
Shugaba Jonathan tun yaushe ’yan Boko Haram ke karbar garuruwa a Jihar Barno, amma ba ka dauki mataki ba? Ko sai da suka shiga Adamawa, saboda su PDP ce take mulki? To su ma Allah zai ba su kariyarSa. Daga Isa Sani Mai arsenal, Garkon Alli 08098556450.
Wuju-wuju alheri ne
’Yana salin Jihar Kano, mun mori Gwamna, irin ayyukan da ake yi a Kano yanzu suka sa muke yabon Marigayi Rimi da Audu Bako. Tabbas idan Kwankwaso ya gama mulki sai mun yaba masa. Daga kanwar Maikawo 0907879664.
Ga Hon. Isa Ashiru
Don Allah Edita ka mik amin sakon fatan alheri ga dan takarar Gwmanan Kaduna a karkashin tutar jam’iyyar APC, Hon. Isa Ashiru Kudan. Daga 08132187415.
Hattara da miyagu!
Salam. Edita. Ina kira ga jama’a da a yi hankali da miyagun malamai, wadanda ke karyar cewa su aljanu ne. Suna nan suna kiran mutane a waya, su umarce su da sayen turare, har ma su rik akawo musu ayar kur’ani da Hadisin Manzon Allah (SAW). Al’umma sia a yi hattara. Daga dan Sakkwatawa 09010055445.