Al’ummar Jihar Oyo sun yi wa Shugaba Buhari kyakkyawar tarba

Hada-hadar sufuri da kasuwanci sun tsaya cik a birnin Ibadan a ranar Asabar da ta gabata, lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ayarinsa suka isa birnin don kaddamar da yakin neman zabensa a zango na biyu a Jihar Oyo. A yayin da direbobi suka yi amfani da motocinsu wajen kwasar dimbin magoya bayan Jam’iyyar […]

Al’ummar Jihar Oyo sun yi wa Shugaba Buhari kyakkyawar tarba

Cincirindon jama’a suna yi wa Shugaba Buhari maraba a Ibadan

Hada-hadar sufuri da kasuwanci sun tsaya cik a birnin Ibadan a ranar Asabar da ta gabata, lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ayarinsa suka isa birnin don kaddamar da yakin neman zabensa a zango na biyu a Jihar Oyo.

A yayin da direbobi suka yi amfani da motocinsu wajen kwasar dimbin magoya bayan Jam’iyyar APC kyauta zuwa babban zauren taro na Mapo da ke tsakiyar birnin mafi girma a Nahiyar Afirka, inda aka kaddamar da yakin zaben, su kuma ’yan kasuwa a manya da kananan kasuwanni da shaguna da kantuna da ke kusa da zauren taron sun dakatar da hada-hadarsu na tsawon awa 4 da Shugaba Buhari ya yi yana kamfen a jihar.

Wakilinmu ya ce tururuwar mutane da suka hada da tsofaffi maza da mata, sanye da tufafi dauke da hotunan Shugaba Buhari da Mataimakinsa Farfesa Osibanjo, sun yi ta rera wakokin “Buhari muke so, Buhari za mu zaba a zabe mai zuwa da Sai Baba!” Wadansu sun yi ta kokarin kutsawa cikin cincirindon mutane ne domin kawai su hango Shugaba Buhari, kamar yadda wata tsohuwa ta daga hannayenta sama tana godiya ga Allah da ya sa ta samu ganinsa a lokacin da ya sauko cikin fara’a rike da tsintsiya yana yi wa jama’a barka a kan hanyarsa ta zuwa garin Osogbo, domin kaddamar da kamfe a Jihar Osun.

Tun farko Shugaba Buhari ya yi wa dimbin magoya bayansa jawabin cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali ne wajen gudanar da muhimman ayyukan gina hanyoyin mota da jirgin kasa na Legas zuwa Ibadan da za a kammala su a karshen bana. Ya ce “Na shaida wa gwamnoninku na wannan sashi na Kudu maso Yamma su koma gona domin ayyukan gona suna da muhimmanci a wannan kasa. Yanzu mun hana shigowa da shinkafa daga ketare inda muka samu ajiye miliyoyin Dalar Amurka da muke gudanar da muhimman ayyuka da su. Za mu ci gaba da yin ayyukan hanyoyi da samar da wutar lantarki. Ina tabbatar muku cewa, za mu cimma wannan buri ne da hadin kanku.”

Cikin jawabin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole, kira ya yi ga ’yan Najeriya su yi amfani da katin zabensu wajen tabbatar da murkushe Jam’iyyar PDP kwata-kwata da dan takararta Atiku Abubakar, wanda a cewarsa yake so ya yi gwanjon kadarorin Najeriya domin sayarwa ga abokansa idan ya yi nasara a zaben 16 ga watan gobe.

Daraktan Yakin Zaben Buhari, Cif Rotimi Amaechi da mai masaukin baki, Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo da Gwamnan Jihar Legas Akinwunmi Ambode da Kayode Fayemi na Jihar Ekiti da Ministan Sadarwa Adebayo Shittu da makamantansu suna daga cikin ayarin Shugaban Kasar  wanda ya fara yada zango a babban zauren taro da ke sakatariyar gwamnatin jihar, inda Alaafin na Oyo Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi da Olubadan na Ibadan Oba Saliu Adetunji suka jagoranci sarakunan gargajiya na jihar da suka yi musu marhabin.