Al’ummar Jos sun gaji da zaben jam’iyyun adawa – dankurma
Tsohon Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Filato kuma jigo a Jam’iyyar PDP a karamar Hukumar Jos ta Arewa Alhaji Auwalu Shehu Maihula dankurma ya ce al’ummar Jos sun gaji da zaben jam’iyyun adawa a zaben Gwamnan Jihar domin yin haka ya cutar da su a baya, saboda haka a wannan karo za su zabi Sanata […]
Tsohon Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Filato kuma jigo a Jam’iyyar PDP a karamar Hukumar Jos ta Arewa Alhaji Auwalu Shehu Maihula dankurma ya ce al’ummar Jos sun gaji da zaben jam’iyyun adawa a zaben Gwamnan Jihar domin yin haka ya cutar da su a baya, saboda haka a wannan karo za su zabi Sanata GNS Pwajok ne na Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa.
Alhaji Auwalu dankurma ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, ind ya ce a yanzu mutanen Jos kansu ya riga ya waye, sun gaji da bin jam’iyyun adawa domin sun yi jam’iyyun adawa ba sau daya ba sau biyu ba, a wajen zaben Gwamna, amma babu nasara.
Ya ce an yaudari mutanen Jos a jam’iyyar adawa a lokacin Gwamna Dariye suka dauki kuri’unsu suka bai wa Alhaji Bello Abdullahi, su kuma mutanen karamar hukumarsa ta Kanam suka ki zabensa suka zabi
Gwamna Dariye ya ci zaben. Ya ce an sake yaudarar mutanen Jos suka sake daukar kuri’unsu suka zabi Mista bictor Lar a zaben Gwamnan Jihar, amma al’ummarsa na karamar hukumarsa ta Langtang suka ki
zabensa suka zabi Gwamna Jang. Har ila yau ya ce an sake yaudararsu suka sake daukar kuri’unsu suka bai Misis Pauline Tallen suka ki zaben Jonah Jang amma al’ummar karamar hukumar Misis Tallen na Shendam suka ki zabenta, suka zabi Jang.
Alhaji Auwalu dankurma ya ce sakamakon wannan yaudara da aka yi wa mutanen Jos suka zabi jam’iyyun adawa a baya, babu hanyoyin mota da ruwan sha a garin.
Ya ce, “Don haka a wannan karo za mu zabi dan takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP, Sanata GNS Pwajok wanda haifaffen garin Jos ne. Ba mu taba samun wannan dama ta samun dan takarar Gwamna a jam’iyyar da ke mulki a garin Jos ba, sai a wannan lokaci. Don haka mun karbe shi hannu bibbiyu kuma da yardar Allah shi ne zai lashe zaben Gwamnan Jihar.”