Al’ummar Kebbi ta Arewa na bukatar sabon wakili a Majalisar Dattawa

Al’ummar mazabar Kebbi ta Arewa da ke Jihar Kebbi sun yi kira ga dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Arewa da Dandi Dokta Hussaini Suleiman Kangiwa da ya yi wa Allah ya karbi kokensu ya fito takarar Sanata ta kebbi ta Arewa wanda ya kunshi kananan hukumomin Argungu, da Augie, da Dandi, da Suru, […]

Al’ummar Kebbi ta Arewa na bukatar sabon wakili a Majalisar Dattawa

Al’ummar mazabar Kebbi ta Arewa da ke Jihar Kebbi sun yi kira ga dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Arewa da Dandi Dokta Hussaini Suleiman Kangiwa da ya yi wa Allah ya karbi kokensu ya fito takarar Sanata ta kebbi ta Arewa wanda ya kunshi kananan hukumomin Argungu, da Augie, da Dandi, da Suru, da Bagudu da Arewa A shekarar 2019 don yankin ya samu tafiya kafada-kafada da sauran yankunan Jihar Kebbi da suka cigaba ta fuskar tattalin arziki da wanzuwar dimokradiyya ga al’ummar su.

Shugaban kungiyar matasa Bagayafo Alhaji Bashir Isa Wazirin Mera ne ya yi wannan kiran a lokacin da al’ummar mazabar Kebbi ta Arewa suka shirya wani gaggarumin taro a garin Kangiwa domin nuna bukatarsu ga dan Majalisar Wakilai Dokta Hussaini Kangwa.

Alhaji Bashir Isa Wazirin Mera, ya ce Dokta Hussaini Suleiman Kangiwa kasancewarsa tun kafin ya shiga siyasa yana rike da mukamin kwanturola na Kwastan yake kyautata wa al’ummar yankin musamman wajen samar wa matasa ayyukan yi da kuma kawo wa a’ummar yankin abubuwan more rayuwa.

Shugaban kungiyar ya ci gaba da cewa manyan mutanen wannan yanki na Kebbi ta Arewa sun zauna sun yi karatun ta natsu cewar tunda Dokta Hussaini Kangiwa ya zama dan Majalisar Wakilai ba a taba samun wani dan siyasa ba wanda al’ummar yankin suka karu da shi ba kamarsa, ya kuma ce tun da aka kirkiro Jihar Kebbi anyi sanatoci a wannan yankin harzuwa wannan lokaci da muke ciki amma ba wanda ya kama kafar Dokta Hussaini Kangiwa wajen kyautatawa al’ummar yankin.

Saboda hakane suka ga ya dace ya bar kujerar Majalisar Wakilai ya tsaya takarar sanata, domin duk dan siyasa da ya yi abin kwarai al’ummarsa na so ya ci gaba saboda karuwarsu ne, amma idan dan siyasa ba shi da amfanin komai ga al’ummarsa, abin da ya kamata shi ne ya dawo gida ya zauna tare da su.

A nasa jawabin, Dokta Hussaini Suleiman Kangiwa cewa ya yi shi ya rasa abin da zai fada, sai dai fatar duk abin da zai zama alheri ga al’ummar wannan yankin Allah Ya tabbatar da shi, sannan ya idan Allah Ya yarda za su je su zauna da duk wani mai ruwa da tsaki na wannan yanki, saboda haka yana neman su ba shi lokaci.

Ya kuma yi godiya ga dukan wadanda suka samu damar halartar wannan taro da wadanda ma ba su samu damar zuwa ba.