Ana zargin gwamnatin Taraba da shirin rushe masallaci mai shekara 112
Sarakunan Kutep waɗanda suka karɓi Musulinci ne suka gina Masallacin Juma’a na garin Takum a cikin shekarar 1912.
Ƙungiyar ’Yan Ƙabilar Kuteb da ke garin Takum a Jihar Taraba sun yi zargin cewa gwamnatin jihar tana shirin rushe Fadar Mai Martaba Ukwe tare da babban masallacin Juma’a da ke garin Takum, wanda aka gina sama da shekaru 110 da suka gabata.
Shugaban Ƙungiyar ’Yan Ƙabilar Kuteb ta Ƙasa, Mista Emmanuel Ukwen ya bayyana cewa ’yan ƙabilan Kuteb ba za su amince da shirin gwamnatin na rushe fadar Ukwe ba wanda nan ne sarakunan Kutep waɗanda suka shafe shekaru aru-aru suna mulki a masarautar Takum ba.
Ya shaida wa ’yan jarida a lokacin wani taron manema labarai a garin Jalingo cewa an ga wani bature tare da jami’an tsaro waɗanda suka haɗa da ’yan sanda da sojoji suna aunawa tare da shafa fenti a fadar ta Ukwe da Babban Masallacin Juma’a na garin Takum wanda ga dukkan alamu rushewa gwamnatin Jihar Taraba take so ta yi.
Ya ce akwai Sarakunan Kutep waɗanda suka rasu aka rufe su a cikin Fadar ta Ukwe saboda haka ba za su amince a rushe fadar ba.
Ya ce fadar ta Ukwe tana ɗauke ne da mihimman abubuwa na tarihi na ’yan ƙabilan Kutep don haka kowa ya san ba wata ƙabilan ko al’umma da za ta yarda a lalata mata kayan tarihinta.
Ya ƙara da cewa sarakunan Kutep waɗanda suka karɓi Musulinci ne suka gina Masallacin Juma’a na garin Takum a cikin shekarar 1912.
Mista Emmanuel Ukwen, ya bayyana cewa garin Takum ya yi fama da rashin zaman lafiya wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka da dukiya mai yawa.
Ya ce su ’yan ƙabilar Kuteb ba sa son a sake samun fitina a garin Takum domin sanin irin yawan asarar rayuka da aka yi a baya.
Ya ƙara da cewa rushe fadar Ukwe tare da Masallacin Juma’a zai iya kawo babban fitina a garin na Takum. Wannan shi ya sa suke jawo hankalin gwamnatin jihar da ka da ta rushe fadar ko masallacin.
Ya ce tuni ma suka shigar da ƙara a gaban kotun ɗaukaka ƙara a garin Yola ta Jihar Adamawa kan kare mutuncin sarautarsu ta Kutep inda suke ƙalubalantar gwamnatin jihar kuma a cikin ƙarar a kwai maganar fadar Ukwe tare da masallacin Juma’ar.
Mista Emmanuel Ukwen, ya nuna damuwar ’yan ƙabilan Kuteb ganin cewa ƙarar tana gaban kotu amma sai ga shi gwamnatin jihar ta yunƙuro da shirin rusa fadar Ukwe tare da masallacin Juma’ar.
Ya ce wannan ya nuna cewar gwamnatin Jihar Taraba ba ta yin biyayya ga umurnin kotu.
“Mu masu biyayya ne ga umarnin kotu kuma muna son zaman lafiya, amma ga dukkan alamu Gwamnatin Jihar Taraba ba ta bin umarnin kotu kuma ita gwamnatin tana son kawo fitina,” in ji Emmanuel Ukwen.
A cewar ’yan ƙabilar Kuteb sun shawarci jami’an tsaro da su hana gwamnatin jihar rushe fadar Ukwe ko Babban Masallacin Juma’an domin magance kawoce irin fitina da rashin zaman lafiya a garin na Takum.
Labarin ƙanzon kurege ne — Gwamnati
Gwamnan Jihar Taraba Agbu Kefas ya ƙaryata wannan zargi na cewa gwamnatin jihar na yunƙurin rushe fadar Ukwe da masallacin Juma’a na garin Takum.
Kwamishinar Yaɗa Labarai na Jihar Taraba, Zainab Usman Jalingo ta ce, wannan zargi ne marar tushe domin babu wani shiri da gwamnatin jihar take yi na rushe tsohuwar fadar Ukwe ko masallacin na garin Takum.
Ta bayyana cewa gwamnatin Jihar Taraba a ƙarƙashin shugabancin Gwamna Agbu Kefas, tana ƙara tabbatar wa jama’a cewa su kwantar da hankalinsu, babu wani shiri mai kama da wannan.
Zainab ta ƙara da cewa wannan labari ne na ƙanzon kurege da wasu ɓata-gari ke bazawa domin jefa fargaba a tsakanin jama’a da nufin tayar da zaune tsaye a tsakanin al’umma.
“Ƙudirinmu shi ne yin ayyuka da za su kawo ci gaban al’umma Jihar Taraba ba tare da la’akari da addini ko ƙabilarsu ba.
“Wannan labarin ƙarya da masu annamimanci ke bazawa, ba zai ɗauke hankalinmu ba daga wannan niyyar tamu. Don haka ina kira da jama’ar Jihar Taraba da su yi watsi da shi,” in ji ta.