Al’ummar Lame za su tura matasa 200 karatun aikin jinya

Al’ummar yankin Lame da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi sun daura damarar rage matsalar karancin ma’aikatan jinya da na ilimi a yankin ta hanyar taimakon kai-da-kai. Hakimin Lame kuma Sarkin Yakin Bauchi Alhaji Aliyu Yakubu Lame ne ya bayyana haka bayan kammala rangadin yankin Tama da Tulu da ke masarautarsa. Ya ce Allah […]

Al’ummar Lame za su tura matasa 200 karatun aikin jinya

Al’ummar yankin Lame da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi sun daura damarar rage matsalar karancin ma’aikatan jinya da na ilimi a yankin ta hanyar taimakon kai-da-kai.

Hakimin Lame kuma Sarkin Yakin Bauchi Alhaji Aliyu Yakubu Lame ne ya bayyana haka bayan kammala rangadin yankin Tama da Tulu da ke masarautarsa. Ya ce Allah Ya yi wa yankin arzikin jama’a, kuma da dama an giggina makarantu da asibitoci amma rashin hanya ya maida yankin baya domin al’ummar na fama da karancin likitoci da ma’aikatan jinya da malaman makaranta saboda da an kai mutum sai ya nemi a yi masa sauyin wurin aiki ya koma birni.

Ya ce duk da yawan jama’ar garin Gumau ma’aikaciyar jinya daya ce ke kula da su, inda ya ce “Ka san akwai matsala, ko ni Hakimin Lame zan iya kamuwa da rashin lafiya, kuma duk lokacin da aka samu marar lafiya in ya fi karfin malamar jinyar sai dai a kai mutum Toro.”

Sarkin Yakin Bauchin ya ce saboda haka yanzu za su tura mutum 200, 40 daga kowace gunduma domin su koyi karatun aikin jinya da nufin rage matsalolin ma’aikatan jinya a yankin, “Kuma daga cikin mutum 200 da za mu tura, har mun samu wanda ya dauki dawainiyar karatun mutum 20 daga cikinsu sauran kuma muna kan kokari,” inji Hakimin.

Ya gode wa Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed kan himmarsa ta aikin hanyar Magama Gumau zuwa Rishi da Rahama, inda ya bukaci al’ummarsa su taya Gwamnan da addu’a ya samu nasarar yin wannan hanya su kuma zauna lafiya da junansu.

Na ƙi biyan kuɗin fansar ’yan uwana sun kuɓuta — Gwamnan Zamfara

Ma’aikatan Abuja ba sa sona — Wike

Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da ofishin ’yan sanda

Gwamnati ta ƙara albashin sojoji — Ministan Tsaro