Al’ummar Mafa sun tsallake harin Boko Haram
A karshen makon jiya ne mutanen da ake zaton ’yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari ga wasu kauyukan da ke karamar Hukumar Mafa a Jihar Borno inda suka kashe akalla mutum 10, tare da yinawon gaba da dabbobi, kuma akasarin mutanen yankin suka yi hijira garin Maiduguri mai nisankilomita 45.Malam Bulama Algoni, daya […]

A karshen makon jiya ne mutanen da ake zaton ’yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari ga wasu kauyukan da ke karamar Hukumar Mafa a Jihar Borno inda suka kashe akalla mutum 10, tare da yin
awon gaba da dabbobi, kuma akasarin mutanen yankin suka yi hijira garin Maiduguri mai nisan
kilomita 45.
Malam Bulama Algoni, daya daga cikin mutanen da suka gudo zuwa Maiduguri, ya ce ’yan Boko Haram sun shigo cikin garinsu su shida a kan babura uku dauke da bindigogi, suka hada su a cikin masallaci suka bude musu wuta.
Ya ce jin haka sai wasu suka ruga da gudu, to amma sai shi ya tsaya daya daga cikinsu ya tsaya kamar zai harbe su, sai can mutanensa suka kira shi suka ce kada ya harbe su, sai suka hadu suka juya suka tafi suka kora musu shanu, inda wasu shanun suka watse zuwa bayan gari. “Shi ke nan sai na mike da yake ni ne Bulaman garin, na ce duk mutanen su watse kada su kara zuwa su same mu su kashe mu, domin sun kashe mutane da dama, daga nan sai kowa ya kama hanyar zuwa Maiduguri, kuma ka gani akasarin mutanen da muka taho da su mata ne da kananan yara a cikin wani mummunan yanayi don haka muke rokon gwamnati ta taimaka mana da abinci da matsuguni,” inji shi.
Malam Modu Goni, ya ce bayan kashe mutane ’yan Boko Haram din sun kwashe garke uku na shanu da dimbin awaki, sannan sun kwace kudaden wadanda suka tsira da ransu.
Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), Injiniya Satomi Alhaji Ahmadu ya ce ’yan gudun hijirar da suka fito daga kauyuka biyar na karamar Hukumar Mafa su 450, za a samar musu da matsuguni da abinci. “Yanzu haka an fara tantance su kafin a bude musu sansani ta yadda za su samu saukin rayuwa,” inji shi.