Al’ummar Mambila ku zauna lafiya da junanku
Assalamu alaikum. Barka da wannan lokaci mai albarka da fatan dukanin ma’aikatan jaridar Aminiya suna cikin koshin lafiya. Da wannan nake son ku ba ni dama domin na yi kira ga al’ummar tsaunin Mambila kan su zauna lafiya da junansu domin samun arziki mayilwaci. Hakika sau da yawa a duk lokacin da wani rikici ya […]
Assalamu alaikum. Barka da wannan lokaci mai albarka da fatan dukanin ma’aikatan jaridar Aminiya suna cikin koshin lafiya. Da wannan nake son ku ba ni dama domin na yi kira ga al’ummar tsaunin Mambila kan su zauna lafiya da junansu domin samun arziki mayilwaci. Hakika sau da yawa a duk lokacin da wani rikici ya tashi, dimbin jama’a ne suke rasa rayukansu, hadi da dukiyoyi, musamman rikici a tsakanin Fulani makiyaya da manoma.
Ko shakka babu, abin takaici ne irin yadda zaman lafiya ya yi karanci a yankin duk da dimbin jami’an tsaron da ake fada ana jibgewa a yankin na tsaunin Mambila. A tsaunin Mambila wani waje ne da a duk lokacin da rikici ya tashi, to abin ba kyan gani. Dubi irin yadda shanu ke mutuwa da mutane babu adadi.
Ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya kara kaimi wajen jibge jami’an tsaro a yankin, kuma a ba su kayan aiki na musamman domin shiga lungu da sako don samar da tsaro a yankin baki daya,
Duk wani yunkurin samar da zaman lafiya da ake so, hakan ba zai yiwu ba har sai mutanen yankin sun kai zuciyoyinsu nesa, wajen ba da kai bori ya hau. Su hada kansu wajen ganin an samar da zaman lafiya domin ci gaban Jihar Taraba, hadi da yin addu’o’in neman zaman lafiya a wajen Allah Mabuwayin Sarki.
Mummunan harin da aka kai tsaunin Mambila ya yi matukar muni kuma hakan ba ci gaba ba ne illa ci baya. Zaman lafiya shi ne ginshikin samar da duk wani ci gaban rayuwa a duniya. Bisa ga haka muke rokon Gwamnatin Jihar Taraba ta yi duk mai yiwuwa domin ganin ta samar da tsaro mai inganci a yankin. Sannan ya kamata a yi binciken kwakwaf don zakulo wadanda suke haddasa rikicin don a hukunta su.
Rikici a Najeriya babu inda zai kai mu, zaman lafiya muke so don ci gaban kasarmu, domin wannan shi ne burin duk wani dan kasa nagari kuma mai kishin kasar.
Ba mu yarda da tashin hankali ba, Najeriya kasa daya ce babu bambanci. Wannan ne ya sa a kullum muke dukufa wajan yi mata addu’ar samun zaman lafiya mai dorewa a kowane yanki na kasar nan.
Ya Allah muna rokonKa Ka ci gaba da kare Najeriya daga dukan wani sharri. Allah Ka ba mu lafiya da zaman lafiya baki daya.
Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau, dan kishin marasa galihu, 08133376020/08086679022