Al’ummar Maya-maya sun koka kan rushewar makarantar Islamiyyarsu

Al’ummar kauyen Maya-maya da ke Karamar Hukumar Dutse sun koka kan rashin makarantar Islamiyya na tsawon shekaru, inda suka ce ’ya’yansu na yin karatu ne a karkashin bishiya. Shugaban Makarantar Ta’alimul Kur’an Walhadis Islamiyya da ke kauyen, Malam Nuhu Hussaini, ya ce saboda rashin kulawar hukumomi tsawon shekara uku dalibansa ke karatu a karkashin bishiya, […]

Al’ummar Maya-maya sun koka kan rushewar makarantar Islamiyyarsu
Al’ummar Maya-maya sun koka kan rushewar makarantar Islamiyyarsu

Al’ummar kauyen Maya-maya da ke Karamar Hukumar Dutse sun koka kan rashin makarantar Islamiyya na tsawon shekaru, inda suka ce ’ya’yansu na yin karatu ne a karkashin bishiya.

Shugaban Makarantar Ta’alimul Kur’an Walhadis Islamiyya da ke kauyen, Malam Nuhu Hussaini, ya ce saboda rashin kulawar hukumomi tsawon shekara uku dalibansa ke karatu a karkashin bishiya, sai ya bukaci gwamnati da al’ummar Jigawa su taimaka musu da kayan karatu da gina makarantar.

Malamin ya nuna damuwa kan yadda rashin wurin karatu yake yi wa makarantar barazana tsawon lokaci, musamman lokacin damina da lokacin sanyi.

“Mun sanar da Karamar Hukumar Dutse da dan Majalisar Dutse, Musa Sule Dutse da dan Majalisar Tarayya, Alhaji Kyanba Madobi amma babu abin da aka yi mana tsawon shekara uku da suka shude. Amma tun da mun yi iyakacin iyawarmu babu wanda ya taimake mu, to idan zabe ya zo za mu yi amfani da karfin kuri’unmu kamar yadda dokar kasa ta ba mu dama. Koda yake Musa Sule ya gina mana masallaci, amma ba shi ne bukatarmu ba a halin yanzu,” in ji shi

Ya ce makarantar ta fara da malami daya da dalibai 13, amma yanzu suna da malamai sama da 13 da dalibai 200, amma ya ce a yanzu matsalar ita ce ba su da makaranta da za su tsugunar da yaran.

Malam Nuhu ya ce suna da yawan masu zabe, amma muddin aka ki yi musu makarantar babu makawa za su kaurace wa zaben da za a yi nan gaba.

Shi ma Mai unguwar kauyen na Maya-maya, Malam Usman Mai Unguwa ya ce kauyensa yana da gidaje sama da 246, kuma sun jima suna fama da matsalar hanya da ruwan sha da rashin wutar lantarki. Ya ce amma abin da ya fi damun mutanen yankinsa shi ne rushewar makarantar Islamiyyarsu tsawon shekara uku saboda ginin kasa ne kuma babu wanda ya taimake su.

Mai Unguwar ya bukaci Karamar Hukumar Dutse ta taimaka musu wajen gina rayuwar ’ya’yansu domin sai da ilimin addini ake yin sallah da sauran ibadoji, yana mai cewa ba masallaci ne damuwarsu ba, makaranta ce.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Shugaban Karamar Hukumar Dutse Malam, Adamu Rungumau, amma Kakakinsa, Malam Jidawa ya ce aikin gina makarantun Islamiyya ba na karamar hukuma ba ne. Amma duk da haka a cewarsa akwai yiwuwar duba matsalolin makarantar.