Al’ummar Mubi sun ji dadin komawar sarkinsu
A Juma’ar da ta gabata ce mai martaba Sarkin Mubi Alhaji Abubakar Isa Ahmadu ya koma garin Mubi, bayan sojoji sun karbi ikon garin daga hannun ’yan Boko Haram.Aminiya ta gano cewa sarkin ya tafi kasar Saudiyya ne tare Amirul-Hajj na Jihar Adamawa, a lokacin da ’yan bindiga suka karbi garin kwanakin baya. Koda ya […]
A Juma’ar da ta gabata ce mai martaba Sarkin Mubi Alhaji Abubakar Isa Ahmadu ya koma garin Mubi, bayan sojoji sun karbi ikon garin daga hannun ’yan Boko Haram.
Aminiya ta gano cewa sarkin ya tafi kasar Saudiyya ne tare Amirul-Hajj na Jihar Adamawa, a lokacin da ’yan bindiga suka karbi garin kwanakin baya. Koda ya dawo ana cikin artabu da ’yan bindigar a Mubi, don haka sai ya tsaya a Yola tsawon lokacin da fadan ya lafa. Wasu daga jami’an Gwamna Ngilari tare da jagorancin Chubado Bamti ne suka raka sarkin zuwa fadarsa da ke garin Mubi.
Mazauna garin Mubi sun yi marhabin da dawowar Sarkinsu, domin tun da aka karbi garin, wannan shi ne karo na farkon da kafarsa ta taka fadar tasa.
Da yawa daga cikin wadanda suka tarbi sarkin, suna fadin “Baba ya dawo,” wanda haka ke nuna tsabagen farin cikin da suka tsinci kansu a ciki. Kuma sun yi addu’ar Allah Ya takaita musu wannan masifar a haka. Kamar yadda Hauwa Umar ta ce: “Dawowar Sarki garin Mubi, alama ce ta nuna cewa kwanciyan hankali da zaman lafiya ya dawo garin.”
Bayan dawowarsasarkin ya je masallacin Juma’a, ya yi Salla tare da mutanen garinsa. Ya kuma yi wa mabiyansa jawabi cewa su dauki duk abin da ya faru da su a matsayin jarabawa ce daga Allah.
“Mu ’yan Najeriya, ya kamata mu yi tunani, mu binciki kanmu a inda muka yi kuskure. Allah zai taimaki duk wanda ya kasance mai yin gaskiya.” Inji shi.