Al’ummar Musulmi sun gudanar da Maulidi a Ibadan
Al’ummar Musulmi a birnin Ibadan sun gudanar da bikin maulidin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen talikai Annabi Muhammadu (SAW). An gudanar da bukukuwan ne a ranar Asabar da ta gabata, wacce ta yi daidai da ranar 12 ga watan Rai’ul Awwal 1439 Bayan Hijira. Birnin na Ibadan ya cika makil da Musulmi maza da mata […]
Al’ummar Musulmi a birnin Ibadan sun gudanar da bikin maulidin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen talikai Annabi Muhammadu (SAW).
An gudanar da bukukuwan ne a ranar Asabar da ta gabata, wacce ta yi daidai da ranar 12 ga watan Rai’ul Awwal 1439 Bayan Hijira.
Birnin na Ibadan ya cika makil da Musulmi maza da mata da kananan yara da suka fito daga sassa daban-daban na Kudu maso yammacin Najeriya, domin halartar bikin na bana.
Kamar yadda aka saba yi a baya, a bana ma shugabanni da malaman makarantun Islamiya ne suka jagoranci daruruwan dalibai maza da mata da kananan yara da matan aure zuwa yin zagayen tafiya a kasa, suna karanto ayoyin Alkur’ani mai girma da salati da wakokin yabon Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) tare da masu kidan bandiri.
A daya bangaren kuma manyan mutane mabiya mazhabobin darikun Tijjaniya da kadiriyya ne suka shiga cikin jerin gwanon da aka faro daga babban masallacin Juma’a na Unguwar Sabo zuwa fadar Sarkin Nufawan Ibadan, Alhaji Shehu Ibrahim da ke Mokola, a inda aka kare wannan tafiyar zagayen a filin wasanni na Lekan Salami da ke Adamasingba, a birnin Ibadan.
Sheikh Umar Abdullahi mai Bandiri, shi ne ya jagoranci mabiya darikar kadiriyya, a yayin da Khalifa Ibrahim Inuwa ya jagoranci mabiya darikar Tijjaniyya wajen yin wannan zagayen da aka gudanar a karkashin jagorancin Alhaji Bashir Khalid.
A yayin da manyan malamai suka yi wa’azin tunatar da Musulmi muhimmancin girmama irin wannan rana, su kuwa shugabannin al’ummomi sun mayar da hankali ne wajen jawo hankalin matasa a game da illar shaye-shayen miyagun kwayoyi da zaman kashe wando.
Shaihunnan malaman sun yi kira ga Musulmi da su yi amfani da dukiyarsu wajen daukar dawainiyar dukkan abin da ya jibinci murnar tunawa da Annabi Muhammadu (SAW). An gudanar da taron zaman wa’azi na yinin wannan rana ne a karkashin shugabancin Tukuran Ibadan Alhaji Aminu Yahya. ’Yan sanda cikin shirin ko-ta-kwana ne suka yi wa Musulmi rakiya daga safiyar wannan rana zuwa yammaci da aka kare bikin lami.