Al’ummar Musulmin Filato na fuskantar wariya – Sarkin Wase
Mai martaba Sarkin Wase da ke Jihar Filato Alhaji Sambo Abdullahi ya ce al’ummar Musulmin jihar, suna fama da matsalolin wariya da danniya a jihar. Mai martaba Sarkin Wase wanda har wa yau shi ne Shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta jihar ya bayyana haka ne a lokacin da tawagar al’ummar Musulmin jihar suka kai […]
Mai martaba Sarkin Wase da ke Jihar Filato Alhaji Sambo Abdullahi ya ce al’ummar Musulmin jihar, suna fama da matsalolin wariya da danniya a jihar.
Mai martaba Sarkin Wase wanda har wa yau shi ne Shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta jihar ya bayyana haka ne a lokacin da tawagar al’ummar Musulmin jihar suka kai wa Gwamnan Jihar Barista Simon Lalong ziyarar gaisuwar Sallah a ranar Litinin da ta gabata a gidan gwamnatin jihar da ke Jos.
Ya ce al’ummar Musulmin Jihar Filato suna cikin matsaloli domin duk wuraren da suka fi lalacewa a jihar a nan ne al’ummar Musulmi suke zaune.
Ya ce “A wurarenmu babu hanyoyin mota, babu ruwan sha, babu wutar lantarki. Kuma an kwace makabartunmu a wurare da dama a jihar. Muna da makabarta a Jos da bukur da Barikin Ladi, amma duk an hana mu yin amfani da wadannan makabartu. A yau idan wani dan uwanmu ya rasu samun wurin binne shi ya zama damuwa a wadannan wurare.”
Sarkin ya an kwace musu Makarantar Tunawa da Marigayi Sardauna da ke garin Jos, sannan mutane kadan ne daga cikin al’ummar Musulmi suke samun aikin gwamnati a jihar.
“Don haka muna rokon wannan sabuwar gwamnati ta Jihar Filato, ta duba wannan hali da muke ciki, musamman ganin irin goyon baya da hadin kan da muka bai wa sabuwar gwamnatin a lokacin zaben da ya gabata,” inji shi.
A jawabin Gwamna Simon Lalong ya yi alkawarin canja abubuwa da dama a jihar, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta nuna bambancin addini ko na kabila ba a wajen gudanar da ayyukan inganta rayuwar al’ummar jihar, kamar yadda ya faru a lokacin gwamnatin da ta gabata.
Ya ce, “Za mu duba wannan matsala ta makabartun da aka kwace wa Musulmi a jihar nan da Makaranatar Tunawa da Sardauna da matsalar hanyoyin mota a wuraren da Musulmi suke zaune. Don haka tuni mun kafa kwamitoci domin duba wadannan matsaloli.”
Daga nan ya mika godiyarsa ga al’ummar Musulmin kan ziyarar gaisuwar Sallah da suka kai masa.