Al’ummar Nijeriya cin buri a kan Janar Buhari ba namu ba ne
Babu shakka halin da muka samu kanmu a Nijeriya na rashin abubuwa da dama musamman tsaro da lafiya da ilimi da kasuwanci da sauransu a kasar nan, suna bukatar komawa ga wanda mallakar tsaro da zaman lafiya da komai yake gurinsa shi ne Allah. ya kamata tunaninmu, ya canja kamar yadda Allah ya kawo mana […]
Babu shakka halin da muka samu kanmu a Nijeriya na rashin abubuwa da dama musamman tsaro da lafiya da ilimi da kasuwanci da sauransu a kasar nan, suna bukatar komawa ga wanda mallakar tsaro da zaman lafiya da komai yake gurinsa shi ne Allah. ya kamata tunaninmu, ya canja kamar yadda Allah ya kawo mana wanda zai iya tafiyar da mulkin Nijeriya bisa gaskiya da adalci Shi ne Janar Muhammadu Buhari. Duk dan kasa nagari yana farin ciki da samun mulkinsa. Hakan ya zo ne bisa gazawar Shugaba mai barin gado da ya shafe shekara shida ba a fuskanci komai, a mulkinsa ba. Al’ummar kasa dole ne kowa ya so canji kuma Allah ya dubi zukatan talakawan kasar ba don halinmuba. ya kawo karshen wancen mulkin. To alhamdulillahi bayan haka dole mu dage da addu’o’i kuma a tashi tsaye domin neman gyara,idan da addu’a to babu abin da ba za a iya samun saukinsa ba. Duk abin da Allah ya kawo komai tsananinsa to yana iya saukake shi.Komai zaluncin mai mulki da magoya bayansa yanzu kuma ya rage namu kowa ya koma ga Allah don gudun irin wandannan matsalolin gwamnatin baya.
Tabbas mun dade muna cewa gyara-gyara, Allah ya tabbatar mana da shi kuma kasa ta samu jajirtaccen miji, to jama’a dole mu yi hakuri da abin da za mu gani cikin wannan mulkin da zarar aka ce Janar Buhari ya karbi wannan mulkin.Ya zama dole idan za a gudanar da gyara sai an sha wuya, ita kuma wuyar da za a sha ta dadi ce ganin yadda kasar ta shiga cikin wani yanayi a shekara 16 a mulkin PDP.Dole ne mu yi hakuri, saboda mafi yawancin al’ummar da suka zabi Buhari kowa yana da irin burin da yake cikin ransa wanda yake so Buhari ya aiwatar a mulkin da zai yi na shekara hudu. Na san Buhari shi kadai ne mutun tilo wanda jama’ar kasa suka yi masa shedar yana son gyara a rayuwarsa. Ya zama dole ga janar Buhari ya san su wane ne a jikinsa kuma su wane aka kafa gwamnati da su, musamman wadannan murhunan biyu kusan su ne gwamnati dole idan mutun yana son ganin hadin kai sai da su koda kuwa Jam’iyyar ku daya da su ko ba daya da su ba. Su ne ‘yan Majalisunmu tabbas ni na san Buhari yana sane da irin mutanen da suka shiga cikin guguwar Sak. suka koma kan kujerinsu kuma tabbas mu talakawan mun riga mun shaida wasunsu da yawansu masu laifi ne ina ganin Buhari sai ya yi da gaske wajen ganin yadda za a yi domin dakile burikansu, da wadanda za a biya kudi ko bin umarnin wasu iyayen gidansu a yi amfani da wasunsu. Da dama wajen kawo tarnaki ga wannan sabuwar gwamnati, wanda duk ba ma fatan wannan ta faru amma fa tilas sai an yi taka tsan-tsan. Kuma dole talakawa mu dage da addu’a domin ita ce maganin komai. kuma shi ne zai hadu da mataimaka nagari masu ba shi shawara. Har ga Allah, ba murna za mu yi ta yi ba idan an yi murnar sai mu zauna mu yi tunani shin ita wannan gwamnati da suwa-da suwa za a kafa ta saboda magance irin badakalar da aka tafi aka bari a kasar. Amma mafi yawancin ‘yan Nijeriya ba ma tunanin haka musamman ‘yan uwana matasa, kawai su ya za a yi su ga an kama wani ko wata da ake zarginsu da sata ko akasin haka wanda ba wannan ne ya kamace mu ba. Shi Buhari ya fi kowa sanin halin da kasar take ciki kuma ya san ta ina zai bullo mata.
Na kara da cewa idan ba ku manta ba, tun bayan da nasarar da madugun guguwar canji Janar Muhammad Buhari ya yi a kan abokin takararsa mai barin gado, nake cin karo da hasashen wasu, daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP suna yi wa Janar Buhari da sauran al’ummar Nijeriya da suka juya wa jam’iyyar ta su baya a zabukan da aka gudanar fatan tsiya da fatan wani jafa’i ya afka wa gwamnati mai jiran gado. An jiyo wasu masu hasashe suna cewa kamar yadda guguwar sauyi ta yi awon gaba da mai barin gado da sauran ‘yan kanzaginsa, to haka guguwar juyin-juya hali za ta yi gaba da gwamnatin Janar Muhammad Buhari mai Jiran Gado! Bakinsu, har suna kafa misali da yadda guguwar sauyi ta yi awon gaba da gwamnatin Misrah karkashin Shugaba Hosni Mubarak wanda Muhammad Morsi, ya hau karagar mulki kuma a karshe ‘yan kasar.
suka sake tuntsurar da gwamnatin Morsi! Kun ji fa, sai dai a fahimtar da na yi wa tawilin wasu daga cikin masu fashin baki da alkalaminsu ya biyo takan wannan matashiya sun bayyana wannan a matsayin hannunka mai sanda ta yadda sabuwar gwamnati za ta yi taka tsan-tsan domin gani ga wane,ya isa wane tsoron Allah.
To amma idan ba fatan wani abu mai kama da wannan ya samu kasarmu ba, me ya hada zaben Nijeriya da juyin-juya-halin kasar Masar? To ko ma dai me ne ne hasashen naku, na san al’ummar Nijeriya sun yi hakurin shekaru aru-aru ana gasa musu aya a hannu wannan bai sanya sun fita sun tumbuke gwamnati ba sai yanzu da suka zabar wa kansu mutumin da duniya ta yi masa kyakkyawar shaida su yi masa boren da zai kai shi ga barin mulki? Allah ya kiyaye, ba shakka wannan ba komai ba ne illa mugun fata da yunkurin yi wa sabuwar gwamnati zagon kasa.
Za mu ci gaba in sha Allah!