Al’ummar Unguwar Rogo sun yunkuro don gyara hanyarsu

Sakamakon abin da suka kira watsi da gyaran hanyoyin uguwannin da al’ummar Hausawa suke zaune a garin Jos, musamman Unguwar Rogo da Unguwar Rimi da gwamnatin Jihar Filato ta yi, al’ummar unguwannin sun fara aikin taimakon kai da kai don gyara hanyarsu.Da yake zantawa da wakilinmu shugaban kwamitin aikin kuma Sakataren Majalisar Malamai ta kungiyar […]

Al’ummar Unguwar Rogo sun yunkuro don gyara hanyarsu
Al’ummar Unguwar Rogo sun yunkuro don gyara hanyarsu

Sakamakon abin da suka kira watsi da gyaran hanyoyin uguwannin da al’ummar Hausawa suke zaune a garin Jos, musamman Unguwar Rogo da Unguwar Rimi da gwamnatin Jihar Filato ta yi, al’ummar unguwannin sun fara aikin taimakon kai da kai don gyara hanyarsu.
Da yake zantawa da wakilinmu shugaban kwamitin aikin kuma Sakataren Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen jihar, Malam Tanimu Aliyu ya ce duk da aikin hanyoyin da ake yi a jihar
Filato an yi watsi da hanyar Unguwar Rogo zuwa Unguwar Rimi, duk da dubban mutanen da suke zaune a unguwannin.
Ya ce hanyar ta koma kamar kwazazzabo saboda ramuka, “tun motoci suna bi har an kai ga sun kasa bin ta, saboda ramukan da hanyar ta yi. An mayar da mu saniyar ware, an ki a gyara mana hanyar,” inji shi.
Ya ce sun yi iyakar kokarinsu don ganin ’yan siyasa su zo su yi musu aikin, amma abin ya gagara. Don haka suka yanke shawarar tashi su taimaki kansu da kansu, su yi aikin gayya don gyara hanyar.
Malam Tanimu Aliyu ya ce sun shirya taron kaddamar da gidauniyar wannan aiki, amma sai gwamnatin jihar ta roki kada a yi taron, za ta zo ta yi aikin. “Don
haka muka dakatar da taron kaddamar gidauniyar, muka ci gaba cike ramukan hanyar. Kafin ranar da gwamnati za ta zo ta yi mana aikin hanyar,” inji shi.
Ya ce sun yi amfani da masallatai da jama’ar unguwa wajen neman gudunmawa don gudanar da aikin kuma ya ce sun yi amfani da kasa mota 60 da duwatsu mota 40. Sai ya yi  kira ga mutanen unguwar su ba da gudunmawarsu gwargwadon hali don a cike ramukan da ke kan hanyar.
Ya yi kira ga gwamnatin Jihar Filato ta yi kokarin gyara hanyar kamar yadda ta yi alkawari, domin mazauna unguwannin talakawanta ne kamar sauran al’ummar jihar.