Amaechi ya ninka kudin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna
Dole fasinja ya mallaki man wanke hannu ya kuma sa takunkumi a koyaushe.
Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya sanar da ninka kudin tikitin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna idan aka dawo da jigilar fasinja.
Ameachi ya ce hakan zai faru ne saboda jiragen za su koma daukar rabin fasinjojin da suka saba dauka, domin tabbatar da bayar da tazara kamar yadda dokar coronavirus ta tanada.
“Kudin zai ninku ne saboda taragon da ke daukar mutum 88 zai koma daular mutum 40, shi ya sa kudin zai karu amma za mu yi magana da Shugaban Kasa kafin lokacin”.
A cewarsa, sabon tsarin hawa jirgin kasa ya wajabta wa kowane fasinja ya mallaki man wanke hannunsa, ya kuma kasance sanye da takunkumi a tsawon tafiyar.
Sai dai bai bayyana lokacin da za a bude sufufin na jirgin kasar ba.
Sabon farashin tikiti
“Muna bukatar bayar da tazara domin tabbtar da ba a samu yaduwar COVID-19 ba. Abu ne mai wuyar sha’ani musamman la’akari da yawan fasinjoji 4,000 da ke bin jirgin a tsakanin Abuja da Kaduna a kullum”, inji shi.
Kafin rufe sufurin bayan bullar cutar coronavirus ana sayar da tikitin babbar kujerar jirgin ne a kan N2,500 zuwa N3,000, karamar kujera kuma N1,300 zuwa N1,500.
Amma a jawabinsa yayin ziyarar gani da ido a kan layin jirgin kasa na Itakpe zuwa Warri, ministan ya ce babbar kujerar za ta koma N5,000 zuwa N6,000, karama kuma N2,600 zuwa N3,000.
Jirgin kasa daga Warri zuwa Itakpe
Ya kuma ce an kammala aikin jirgin kasa da ga Itakpe zuwa Warri, yana mai yabawa da ingancin aikin wanda ya ce nan gaba Shugaba Buhari zai kaddamar.