Aman Naira
Wani Bakatsine ne za shi Hadeja ci-rani, ya tanadi kudinsa har Naira dubu goma. Suna tafiya sai ’yan fashi suka tsare su. To kafin su fito daga motar sai Bakatsine ya cusa kudinsa a baki. Bayan ’yan fashin sun karbe kudaden sauran, mutuminka ya yi gum da baki. An yi, an ya yi magana amma […]
Wani Bakatsine ne za shi Hadeja ci-rani, ya tanadi kudinsa har Naira dubu goma. Suna tafiya sai ’yan fashi suka tsare su. To kafin su fito daga motar sai Bakatsine ya cusa kudinsa a baki. Bayan ’yan fashin sun karbe kudaden sauran, mutuminka ya yi gum da baki. An yi, an ya yi magana amma ya ki. Sai wani dan fashi ya tambaye shi: “Mene ne a bakinka?” Sai ya girgiza kai, alamar ba komai. Kawai sai dan fashin nan ya wanka masa mari, ya kara masa, sai Bakatsine ya zaro dubu daya daga bakinsa, ya mika wa dan fashi. Da suka yi haka sau uku, yana wanka masa mari, shi kwa yana zaro masa dubu-dubu. Sai dan fashin nan ya kira ’yan uwansa, ya ce musu: “Ku zo ga ATM, lambarsa mari kawai.” Ba sai ’yan fashin nan suka yi layi ba, kowa ya zo sai ya wanke Bakatsine da mari. Goganka kuwa sai zaro masa dubu yake. Haka dai har kudin suka kare.
Daga Abdullahi Musa Hadeja, 07066180429