Amare sun fice daga liyafar bikinsu don zuwa rubuta jarrabawar kammala karatu
Wasdanu amare Dorcas Atsea da Deborah Atoh a lokacin da ake tsakiyar bikin aurensu kwatsam sai aka sanar dasu cewa a wannan lokacin za su rubuta jarrabawar kammala karatun jami’arsu. Amaren Dorcas Atsea da Deborah Atoh wadanda dalibai ne da ke karatun fannin aikin jarida a jami’ar jihar Benue, nan take suka fice daga cikin […]
Wasdanu amare Dorcas Atsea da Deborah Atoh a lokacin da ake tsakiyar bikin aurensu kwatsam sai aka sanar dasu cewa a wannan lokacin za su rubuta jarrabawar kammala karatun jami’arsu.
Amaren Dorcas Atsea da Deborah Atoh wadanda dalibai ne da ke karatun fannin aikin jarida a jami’ar jihar Benue, nan take suka fice daga cikin taron jama’ar da suka tara don bikin nasu a daidai lokacin da madaurin auren ke tambayersu cewa, suna son junansu a matsayin ma’aurata kuma za su iya rike amanar juna? Da sauran tambayoyi da kuma sharuddan aure da aka yi a wani coci.
Kawai sai ga sanarwar gaggawa cewa jarrabawar da ya kamata su rubuta ta tun a watan Fabrairu yanzu an mayar ranar 7 ga Afrilu wanda ya yi daidai da ranar auren, bayan duk sun sanar da ranar bikin.
Kafin su fice daga wurin bikin sai da suka canza kayan jikinsu.
Atsea, ya bayyana wa manema labarai cewa an riga an sanya bikin kafin jarrabawar amma mun yi yunkurin a ba mu dama don bayan jarrabawar mu rubuta tamu amma abin ya cutura, don har sai da muka tuntubi malamar gudanar da jarrabawar a karshe sai cewa, ta yi mu zabi aure ko jarrabawa?