Amarya da mai juna biyu sun mutu a gobarar matatar mai a Ribas

Mutum 18 sun mutu, ciki har da wata mai juna biyu da wata amarya, sun mutu sakamakon gobarar matatar man fetur ba bisa ka’ida ba a Jihar Ribas

Amarya da mai juna biyu sun mutu a gobarar matatar mai a Ribas

Wani bututun danyen mai. (Hoto:NNPC)

Mutum 18 sun mutu, cikinsu har da wata mai juna biyu da wata amarya, sun mutu sakamakon fashewar wata matatar man fetur ba bisa ka’ida ba a Jihar Ribas.

Wani jami’in tsaro a yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutane da dama sun kokkone baya ga mutum 18 da suka mutu a sakamakon bindigar da matarar man ta yi.

Mai magana da yawun hukumar tsaro ta sibil difens (NSCDC) a jihar, Olufemi Ayodele, ya ce, “Da tsakar dare wutar ta fara ci … 18 mutum 18 un kone kurmus, wasu 25 da suka samu raunukan kuna kuma an cece su.Ya ce, “Yawancinsu matasa ne… sai wata mai juna biyu da wata mata da ake shirin bikin daurin aurenta a cikin wadanda a bin ya ritsa da su.”Mazauna yakin Emohua sun ce adadin wadanda suka mutun zai iya karuwa saboda akwai wadanda ke kwasar man da ke tafiya a kasa lokacin da gobarar ta tashi.

Wutar ta tashi ne bayan wuta ta kama a rumbun ajiyar mai na matatar, inda ta kokkona mutane, ta kashe washe.

Mazauna yakin Emohua sun ce adadin wadanda suka mutun zai iya karuwa saboda akwai wadanda ke kwasar man da ke tafiya a kasa lokacin da gobarar ta tashi.Matsalar fasa bututun mai da tacewa ba bisa ka’ida ba ta yi kamari a yankin Kudancin Najeriya, inda man da ke gangarawa ta bututun da masu satar man suke amfani da su kan yi bindiga su hallaka mutane.

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta