Amarya da tsohon saurayinta sun yi yunƙurin kashe ango
Dubun wata amarya ta cika bayan da ta haɗa baki da tsohon saurayinta domin kashe angonta.
Dubun wata amarya ta cika bayan da ta haɗa baki da tsohon saurayinta domin kashe angonta makonni kaɗan bayan ɗaurin aure.
A halin yanzu ’yan sanda na tsare da amaryar suna bincikarta bayan ta kashe abokin angon nata a Jihar Jigawa.
Amaryar mai shakara 15, da taimakon tsohon saurayinta, sun haɗa baki wajen sanya wa mijin nata guba a abinci don ya mutu ne, domin ta auri tsohon saurayin nata.
Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa amarya “ta ajiye wa angon nata abincin da guba a ciki ne da nufin kashe shi, amma sai aka yi rashin sa’a ya zo da baƙi da suka zo taya shi murnar auren.
“Bayan sun kammala cin abincin ba su san da gidan a ciki ba, nan take ɗaya daga cikin abokan angon ya rasu, ango da ɗayan kuma cikinsu ya ƙulle aka garzaya da su asibiti, inda aka yi nasarar ceto rayuwarsu.”
Ya yi zargin amaryar ta yi haka ne da nufin ɗaukar fansa da kuma rabuwa da mijin nata mai suna Kamisu Haruna, wanda ba ta son aurensa
Kakakin rundunar ’yan sans a Jihar Jigawa, Lawal Shiisu ya shaida wa Aminiya ranar Asabar cewa, a halin yanzu suna gudanar da bincike kam lamarin da ya faru a ƙauyen Albasu da ke Ƙaramar Hukumar Jahun.
Ya ce bayan an kai waɗanda suka ci abincin asibiti ne aka tabbatar da rasuwar ɗaya abokin angon, amma an yi nasarar ceto rayuwar angon da ɗaya abokin nasa..