Amarya ko madubi?
Wani bakauye ne ya je birni neman kudi, da zai dawo sai ya sawo wa matarsa madubi. Da ya iso gida, ta tare shi cikin murna, sai ya ce mata ya kawo mata tsaraba. Ta yi godiya, sai ya dauko madubin ya ba ta. Ta fara dubawa ke nan sai ta ga fuskarta a ciki. […]
Wani bakauye ne ya je birni neman kudi, da zai dawo sai ya sawo wa matarsa madubi. Da ya iso gida, ta tare shi cikin murna, sai ya ce mata ya kawo mata tsaraba. Ta yi godiya, sai ya dauko madubin ya ba ta. Ta fara dubawa ke nan sai ta ga fuskarta a ciki. Dayake ba ta taba ganin madubi ba, sai ta yi fushi ta yi yaji zuwa gidansu, ta shaida wa mahaifiyarta cewa wai mijinta ya je birni ya yi mata kishiya. Ta kara da cewa wai domin ma ya raina mata wayo shi ne ya kawo mata hoton amaryar don ta gani, wai ya ce tsaraba ce. Uwar ta ce mata ta nuna mata hoton ta gani. Da uwar ta amshi madubi ta duba sai ta ga fuskarta a ciki. Nan take ta ce: “In dai wannan tsohuwar banzar ce ya gani har ta burge shi, sai mun yi maganinta.”
Daga No Sleeping (Ba Ka Barci) Daura 08034679320