Amarya ta farfado bayan an binne ta a kabari
Ta farfado bayan awa 15 da likita ya tabbatar da rasuwarta.
Wata amarya da aka binne kabari bayan likita ya tabbatar da rasuwarta ta farfado bayan wata mas’ala ta sa an tona kabarinta.
Wanna abun al’ajabin ya faru ne a garin Kurfi na Jihar Katsina, kimanin sati biyu kafin daurin auren amarya Sa’adatu, wadda ita da kanta ta raba wa kawayenta kayan baikon da aka kawo mata.
Bayan an binne ta da kusan awa 15 da likita ya tabbatar da rasuwarta ne aka tona kabarin nata aka kuma same ta da ranta idanunta biyu, a safiyar ta Larabar wannan makon.
Al’ummar Layin Tantan da ke garin na Kurfi da suka shaida abin da ya faru da budurwar sun yi wa Aminiya bayanin abin da ya faru dalla-dalla.
– Abin da ya ‘kashe ta’ da farko
Abokin mahaifin Sa’adatu Hassan mai suna Alhaji Rabi’u Aliyu Maifeshi ya shaida wa Aminiya cewa, “Da misalin karfe bakwai na yammacin Talatar da lamarin ‘mutuwar farko’ ta faru shi ne ta wanke kayanta ne, to wajen yin shanya a igiyar da suke yi, abin kaddara, sai ta hado da wayar lantarki. Kafin ace kwabo har ta kai kasa babu rai.
“Nan da nan aka dauke zuwa wani asibiti mai zaman kansa domin ceto rayuwarta.
“Lokacin da aka je can, sai likitan da aka taras bayan sun yi awon da za su yi mata, suka tabbatar da cewa rai ya yi halinsa.
“A takaice bayan an dawo gida an yi mata wanka da duk abin da za a yi har an sanya ta cikin makara.
– Kwanan keso
“Amma saboda dare ya yi aka ce a bari da safe an yi mata janaza —Haka kuma aka yi”.
Bayanan da Aminiya ta samu sun ce bayan da rufe Sa’adatu wajen karfe 8 na safiyar Laraba an dawo wajen zaman makoki, sai wani daga cikin mutanen da suka rufe ta ya ce shi dai har yanzu zuciyarsa ba ta ba shi cewar yarinyar nan ta rasu ba.
Kamar yadda mai maganar ya ce, lokacin da suke sanya ta cikin kabari ya ji cikin ta yayi kuka kuma kamar da alamu har ta yi tusa.
Fadin haka, sai bayanai suka ci gaba da fitowa musamman daga bakunan wasu daga cikin wadanda suka dauke ta a makara zuwa makabarta inda suka ce sun ji wannan kukan ciki gami da yin tusar.
Amma kowanensu ya ce ya yi shiru da bakinsa don gudun faruwar husuma musamman a ce ko wani abu ne na sihiri.
A takaice dai aka yanke shawarar zuwa a tone kabarin don tabbatarwa — haka kuma aka yi.
Ganau sun shaida wa wakilin Aminiya cewa a lokacin da labarin shakkun mutuwar yarinyar ya shiga cikin gidan, sai matan da suka kwana da gawar suka ce, hakika a cikin dare sun rika jin motsi a wajen makarar amma ba su damu ba saboda sun yi zaton ko beraye ne.
An same ta raye
Daga nan ne aka je aka tono gawar Sa’adatu, aka kuma same ta a raye, idanunta a bude, sai yanayin jikinta ya canza, duk ta galabaita.
Nan take aka wuce da ita zuwa Babbar Asibitin garin Malumfashi domin sake ceto rayuwarta a karo na biyu.
Bayan kimanin awa guda a cikin asibitin ana kula da ita Allah Ya karbi ranta.
Ita dai Sa’adatu wadda ke aji biyar a babbar makarantar sakandire, saura sati biyu a daura auranta, ance ita da kanta ta raba wa kawayenta kayan baikon da aka kawo mata.