Amarya ta fasa aure saboda ango bai iya lissafi ba
Wata amarya a kasar Indiya ta fasa auren, saboda angonta ya kasa amsa tamabaya a kan lissafi, kamar yadda jami’an ’yan sanda suka bayar da sanarwa. Wannan amarya ta auna fahimtar angonta, inda ta tambaye shi, nawa ne 15 + 6? Sai ya bata amsa da cewa: 17.Wannan ala’amari ya auku ne a kauyen Rasoolabad […]
Wata amarya a kasar Indiya ta fasa auren, saboda angonta ya kasa amsa tamabaya a kan lissafi, kamar yadda jami’an ’yan sanda suka bayar da sanarwa.
Wannan amarya ta auna fahimtar angonta, inda ta tambaye shi, nawa ne 15 + 6? Sai ya bata amsa da cewa: 17.
Wannan ala’amari ya auku ne a kauyen Rasoolabad da ke kusa da garin Kanpur a Arewacin Jihar Uttar Pradesh, a cewar jami’in ’yan sanda Rakesh Kumar.Iyayenh ango su yi matukar kokarin gnain sun shawo kanta kan ta amince, amma ta ki. Ta ce angon ya yaudareta ta hanyar yin karya game da matsayin iliminsa.