Amarya ta ga tasku a hannun sojoji -Kubutattun ’yan Arewa

Fiye da makonni biyu samari da magidanta ‘yan kasuwa guda 486 suka samu kansu a tsaka mai wuya a garin Abiya ta kudancin Najeriya.  Sun shiga wannan hali ne sanadiyyar kama su da sojoji suka yi da zargin cewa ‘yan ta’adda ne.daya daga cikin ‘yan jihar Jigawa da aka sako su mai suna Shehu, ya […]

Amarya ta ga tasku a hannun sojoji -Kubutattun ’yan Arewa
Amarya ta ga tasku a hannun sojoji -Kubutattun ’yan Arewa

Fiye da makonni biyu samari da magidanta ‘yan kasuwa guda 486 suka samu kansu a tsaka mai wuya a garin Abiya ta kudancin Najeriya.  Sun shiga wannan hali ne sanadiyyar kama su da sojoji suka yi da zargin cewa ‘yan ta’adda ne.
daya daga cikin ‘yan jihar Jigawa da aka sako su mai suna Shehu, ya bayyana wa Aminiya cewa, an kama su ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Ribas domin kai amaryar wani dan uwansu.
Ya ce,’’’Ina cikin mutane bakwai da za su kai amarya wurin mijinta, wanda soja ne da ke zaune a jihar Ribas, sauran matan da aka kama mu tare da su duk suna cikin ‘yan rakiyar amarya ne, domin al’adarmu ce raka amarya zuwa gidan mijinta. Mun yi kokarin yi musu bayani amma sun ki sauraronmu. Yaya kake jin amaryar da aka tsare kwana 13, bayan kwana guda da daura aurenta za ta ji?’’  
Haka kuma Aminiya ta samu ganin mutane 29 wadanda ‘yan asalin jahar Kano ne da aka sako su. A hirarsu da wakilinmu ya yi da wadansu daga cikinsu a yayinda gwamnan jahar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya karbe su, sun bayyana yadda aka kama su da kuma yadda suka shiga tsaka me wuya a hannun sojoji.

Yadda muka samu kanmu a hannun sojoji
Mudashir Aliyu, daya ne daga cikin fataken da aka kama su,ya ce sojoji sun tsaida su ne a daidai lokacin da suke kokarin shiga Fatakwal da misalin karfe 1:30 na dare ranar Asabar 15 ga watan Yuni. “Ni dai na shiga mota ne daga Hotoro NNPC, dama motar ta taho ne daga jahar Jigawa, kuma duk ranar Asabar take zuwa, idan ta zo sai ta dauki fasinjan kano ta hada. Duk gaba dayanmu ‘yan kasuwa ne.’’
Mudasshir,  wanda ya ce shi sana’ar sa saye da gyaran Agogo ne a garin Fatakwal, ya ci gaba da cewa, “A lokacin da muka je Abiya mun tarar sojoji sun tsaida wata mota, muma da muka zo sai suka tsaida mu. Ana ta cewa wai an kama mu a motoci 33 munyi jerin-gwano, to Wallahi karya ne. Sojojin sun tattara mu ne har muka kai wannan adadin na motoci 33. Bayan sun tara mu sai suka ce da mu saboda halin da gari yake ciki mu bari sai karfe 6:00 na safe sai su sallame mu mu tafi. Amma abin mamaki da lokacin ya yi sai kawai muka ga tankokin yaki sun zo sun zagaye mu. Suka shiga cikin motocinmu suna caje mu. A take suka karbe wayoyinmu suka tarkata mu zuwa Barikinsu.”
A lokacin da suke bariki, inji Mudasshir, “an ware mata takwas daga cikinmu da su da ‘ya’yansu, a cikin matar akwai wata amarya ta wani sojan-ruwa za a kai masa tun da a can yake.’’
“Bayan sun kwashe matan, mu 478 maza da muka rage sai suka sanya mu a cikin daki guda daya suka rufe. Sai da mukayi kwana uku a cikin wannan halin, saboda kankantar dakin da suka cusa mu idan dare ya yi wadansu sai dai su tsaya, wadansu kuma su kwanta, idan na kwancen sun dan yi barci, sai na tsayen su tashe su don su ma su dan samu su runtsa. Kuma a kwana ukun nan duk wanda ya ji fitsari ko kashi sai dai ya yi a cikin nan, domin ba a zuwa wajenmu sai karfe biyar ta kowace rana, wato lokacin abinci.”
Ta bangaren abinci kuwa, sojojin suna ba mutanen Alale guda daya ne da ruwa kofi daya a rana. “Akwai lokacin da muka yi kwana biyu, wannan din ma ba mu samu ba. Wannan ya sa wadansu daga cikinmu suka fita daga hayyacinsu. Mun zata da yawa ba za mu rayu ba. A halin yanzu da nake maka magana akwai wani dan jahar Jigawa da ya riga ya haukace gaba daya.”

Neman ‘yan Boko Haram a cikinmu
daya daga cikin wadanda aka kama ya bayyana wa Aminiya cewa a lokacin da suke tare, “an kawo ‘yansanda sun bincike mu,jami’an shige da fice (immigration) ma sun zo sun yi nasu, sannan jami’an tsaro na ciki (SSS) su ma suka yi nasu. Lokacin da ‘yan sandan ciki (SSS) suka zo sun tambaye mu cewa wace irin akida ta musulunci muke bi, kowa sai sun yi masa wannan tambayar. Kuma suna tambayar kowa ko ya taba rike bindiga . Sannan suna duba hannun kowa domin su gane ko ya taba rike bindiga. Inda muka gode Allah shi ne, har suka gama bincikensu babu wanda suka samu da laifi.”   

Yadda aka sake mu
Kafin a salami wadannan  ‘yan kasuwan sai da aka karbi adireshinsu, wadansu ma har da lambar asusun ajiyar kudinsu da ke banki. Wadansu da aka karbe musu kudi an mayar musu, amma wadanda kudin nasu a cikin jakar hannu yake, amma  wadanda kudinsu a hannu yake ba a mayar musu ba, sai dai an mayar musu da kayan da suka shafi carbi da zobe da sauransu.
Daga nan ba a bar fataken  sun ci gaba da tafiyar da suka shirya ba, domin an dawo  da su Arewa aka yi.  Wannan ya sa gwamnatin Kano da ta karbi nata ta ba kowanne daga cikinsu kudin mota N20,000. Mafi yawan fataken sun fito ne daga karamar hukumar Sumaila.
A Jihar Jigawa kuwa, kowa an danka shi ne ga shugaban karamar hukumar da ya fito.
A ranar Talatar da ta gabata ma an sake sako wadansu ‘yan jihar Kano guda 24.
Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya gargadi fataken da su kama sana’a kuma su dauka wannan abu da ya faru a gare su jarrabawa ce daga Allah.