Amarya ta haihu a ranar budar–kai
Wata amarya mai suna Jamila Sule Kargo mai kimanin shekara 16 ta haihu kwana daya da tarewarta a gidan miji a kauyen Limawa ta karamar Hukumar Dutse da ke Jihar JigawLamarin ya sa angonta Malam Muhammed Abdullahi dansabo da ’yan uwansa suka yi wa Jamila korar kare daga gidan zuwa gidan iyayenta da ke kauyan […]
Wata amarya mai suna Jamila Sule Kargo mai kimanin shekara 16 ta haihu kwana daya da tarewarta a gidan miji a kauyen Limawa ta karamar Hukumar Dutse da ke Jihar Jigaw
Lamarin ya sa angonta Malam Muhammed Abdullahi dansabo da ’yan uwansa suka yi wa Jamila korar kare daga gidan zuwa gidan iyayenta da ke kauyan Kargo a karamar Hukumar Dutse inda aka dakatar da bukukuwan aure da sauran maganar biki, gidan ya yi tsit kamar an yi mutuwa.
Kwamandan Hisba na Jihar Jigawa Ustaz Aliyu Galamawa wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni suka kama amaryarsuna ci gaba da bincike a kan lamarin.
Ya ce binciken da jami’an Hisba suka yi sun gano cewa wani matashi mai suna Bilya Rayuwa na kauyen Andaza da ke karamar Hukumar Kiyawa ne ake zargin ya yi mata cikin.
Kwamandan ya kara da cewa sun buga wa wanda aka zargin shi ne ya yi mata cikin a waya lokacin da yake cin Kasuwar Sara, ya ce yana zuwa kuma da zarar sun kama shi za su mika shi ne ga ’yan sanda domin zurfafa bincike a kansa su kuma gurfanar da shi a gaban kotu domin yi masa hukuncin da ya dace.
Ustaz Galamawa ya shawarci iyaye su rika sanya ido a kan ’ya’yansu da kuma shawartar masu niyyar yin aure su rika zuwa asibiti domin yin gwaje-gwajen ciki da na kanjamau da sauransu kafin daurin auren.
Wakilinmu ya yi bakin kokarinsa domin jin ta bakin angon dansabo amma ya ki yin magana, sai dai wata majiya ta ce ya gaya wa ’yan Hisba cewa ya yafe duk abin da ya kashe wa amaryarsa ya yafe ba ya bukatar komai daga wajenta kuma ba ya bukatar a rika yawo da shi zuwa wajen shari’a saboda haka ya sahale mata.