Amarya ta kashe ango mako biyu da yin aure a Kano

Rundunar ‘yan sanda ta cafke wata mata mai suna Sadiya Umar da ake zargi da kasha mininta  mai suna Umar Sani har lahira ta hanyar mako biyu da yin aurensu. Wannan lamarin ya auko ne a rukunin gidaje na Yakasai da ke cikin garin Kano a ranar Alhamis da ta gabata. Ana zargin amaryar ne […]

Amarya ta kashe ango mako biyu da yin aure a Kano

Rundunar ‘yan sanda ta cafke wata mata mai suna Sadiya Umar da ake zargi da kasha mininta  mai suna Umar Sani har lahira ta hanyar mako biyu da yin aurensu.

Wannan lamarin ya auko ne a rukunin gidaje na Yakasai da ke cikin garin Kano a ranar Alhamis da ta gabata.

Ana zargin amaryar ne da kashe mijin nata ta hanyar zuba masa goban kashe bera a cikin abincin da ya ci a ranar Alhamis, sannan ya garzaya barzahu washegari a asibitin koyarwa na Aminu Kano.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano, DSP Magaji Musa Majiya ne ya tabbatar wa wakilinmu aukuwar lamarin ta wayar tarho inda ya ce, “‘yanuwan mamacin ne suka kawo kara a ofishin ‘yan sanda na Kofar Wambai, sannan jami’anmu suka je gidan inda suka samu matar ta arce, amma daga baya suka samu nasarar cafke ta.”