Amarya ta kashe angonta a Bauchi

Amaryar ta daɓa wa angonta wuƙa a ƙirji.

Amarya ta kashe angonta a Bauchi

Wata amarya mai shekaru 21, Maimuna Suleiman ta kashe mijinta Aliyu Muhammad ta hanyar daɓa masa wuƙa a unguwar Ƙofar Ɗumi dake Bauchi.

Kakakin rundunar ƴan sanda na Bauchi, ASP Aminu Gimba Ahmed ya ce lamarin ya faru ne ranar 5 ga Yulin 2023 da misalin ƙarfe 6:00 na yamma.

ASP Gimba ya ce bayan da suka samu labari sun garzaya gidan inda suka ɗauki mijin da matar zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa (ABUTH).

Amarya ta kashe ango kwana biyu bayan daurin aure a Adamawa

Amarya ta kashe Angonta don ta zaci fyade zai mata

Ya ce likitoci sun bincika kuma sun tabbatar mamacin ya rasu ne sakamakon raunin da ya samu a ƙirjinsa, yayin da wacce ake zargin ta samu ƙananan raunuka a cikinta.

Kakakin ƴan sandan ya ce wadda ake zargi ta amsa laifinta.

A yanzu haka dai sashen binciken manyan laifuka na rundunar ƴan sanda na ci gaba da bincike kafin gurfanar da ita gaban kotu.

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan

A tabbatar an mutunta tsarin dimokuraɗiyya a Zaɓen Edo — Tinubu