Amarya ta kashe angonta kwana uku da bikinsu

A ranar Talatar da ta gabata wata amarya mai suna Rahama Hussain ta kashe angonta a Unguwar Darmanawa, karamar Hukumar Tarauni da ke Jihar Kano kwana uku da yin bikinsu. Amaryar mai kimanin shekara 18 ta daddaba wa angonta Tijjani Bashir mai shekara 25 wuka ne a wurare da dama har ya cika da misalin […]

Amarya ta kashe angonta kwana uku da bikinsu
Amarya ta kashe angonta kwana uku da bikinsu

A ranar Talatar da ta gabata wata amarya mai suna Rahama Hussain ta kashe angonta a Unguwar Darmanawa, karamar Hukumar Tarauni da ke Jihar Kano kwana uku da yin bikinsu.

Amaryar mai kimanin shekara 18 ta daddaba wa angonta Tijjani Bashir mai shekara 25 wuka ne a wurare da dama har ya cika da misalin karfe 10:00 na dare.
Aminiya ta gano cewa an daura auren ango da amaryar wadanda ’yan uwa ne a ranar Lahadin da ta gabata.
Kakakin Rundunan ’Yan sandan Jihar Kano, ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin inda ya ce a yanzu haka amaryar tana tsare a hannunsu, suna ci gaba da binciken lamarin.
“Lokacin da muka samu labarin aukuwar lamarin jami’anmu sun yi gagagwar isa gidan inda suka dauki mutumin zuwa Asibitin Malam Aminu Kano inda aka tabbatar da rasuwarsa,” inji shi.
Idan za a tuna a kwanakin baya wata amarya mai suna Wasila Tasi’u ta kashe mijinta da wasu mutanen da ke tare ta hanyar sanya masa maganin bera a abinci a Jihar Kano.