Amarya ta kashe angonta ta hanyar ba shi guba
Al’ummar Unguwar Maisoro a karamar Hukumar Gaya ta Jihar Kano suna ci gaba da jimamin rasuwar wani sabon ango mai suna Umar Sani mai shekara 35 da wasu mutum uku da suka mutu sakamakon cin dan wake da aka zuba masa guba bayan kwana bakwai da tarewar amaryarsa.Rahotanni sun ce amaryar mai suna Wasila Tasi’u […]

Al’ummar Unguwar Maisoro a karamar Hukumar Gaya ta Jihar Kano suna ci gaba da jimamin rasuwar wani sabon ango mai suna Umar Sani mai shekara 35 da wasu mutum uku da suka mutu sakamakon cin dan wake da aka zuba masa guba bayan kwana bakwai da tarewar amaryarsa.
Rahotanni sun ce amaryar mai suna Wasila Tasi’u mai shekara 14 da haihuwa ake zargi da sanya wa angon nata guba a cikin abincin da uwargidanta ta dafa da mijin ya ci tare da wadancan mutane a kofar gida suka ce ga garinku nan.
Majiyarmu ta ce kamar yadda al’adar mutanen garin take idan mutum ya yi karin aure to uwargidansa ce za ta ci gaba da girka abincin gidan zuwa wani lokaci kafin amaryar ta fara girki. “Uwargidan ta yi dan wake a matsayin abincin rana. Bayan ta zuba na maigidan sai amaryar ta lallaba ta shiga dakin girki ta zuba guba a cikin abincinsa. Shi kuma ba tare da ya sani ba sai ya dauki abincin ya fita da shi waje suka ci da makwabcinsa, suka ba wani almajiri da wata yarinya mai tallan taliya,” inji majiyarmu.
Majiyar ta kara da cewa “Ba su jima da kammala cin abincin ba ango da makwabcinsa da almajiri suka fara korafin ciwon ciki mai tsanani inda nan take suka ce ga garinku nan.”
Aminiya ta jiyo cewa lokacin da jama’ar unguwa suka fuskanci abin da ke faruwa sai suka yi hanzarin sanar da ’yan sanda a garin Gaya, inda aka kama dukan matan biyu don gudanar da bincike. Kuma a lokacin ne amaryar ta ce ita ce ke da alhakin zuba guba a abincin da ya kashe angonta.
Yarinya mai tallar taliya da aka sam mata dan waken na kwance a asibiti suna jinya.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce Kwamishinan ’Yan sandan jihar zai gana da manema labarai a kan batun da zarar sun kammala bincike.