Amarya ta kashe Angonta don ta zaci fyade zai mata

Amaryar nan da ake zargi da kashe mijinta, Salma Hassan, ta ce ta kashe shi ne da wuka a lokacin da ta ke kokarin kare kanta bayan da ya nemi yin saduwar aure da ita. Ta ce ba ta da masaniyar cewa saduwar aure wajibi ne kuma ginshiki ne a aure, dan haka ta zaci […]

Amarya ta kashe Angonta don ta zaci fyade zai mata

Amaryar da ake zargi da ksahe minjinta

Amaryar nan da ake zargi da kashe mijinta, Salma Hassan, ta ce ta kashe shi ne da wuka a lokacin da ta ke kokarin kare kanta bayan da ya nemi yin saduwar aure da ita.

Ta ce ba ta da masaniyar cewa saduwar aure wajibi ne kuma ginshiki ne a aure, dan haka ta zaci Angon nata ya yi yunkurin yi mata fyade ne ya lalata ta, kwanki 11 da daura auren su.

“A rana ta 11 da auren mu, ya tunkare ni da nufin kwanciyar aure da ni, sai na ki amincewa domin ban taba yin irin wannan abun ba, sai ya fusata ya fara duka na.

“Da na ga haka sai na dauki wuka domin na tsorata shi, sai ya nemi ya sadu da ni ta karfin tsiya ni kuma na caka masa wukar a kirji.

“Ban yi niyyar kashe shi ba, na kuma yi nadamar abun da na yi”, in ji ta.

Salma Hassan ta bayyana haka ne a lokacin da rundunar ‘yan sandan Bauci ta gabatar da ita ga manema labarai tare da karin wadanda ake zargi da laifuka dabam-daban su 21, ciki har da masu garkuwa da mutane.

A cewar Kwamishinan ‘yan sandan jihar  Bauchi Philip Maku, an kama Amaryar da ake zargi da kashe mijinta tare da wukar da ta aika ta laifin, a gidan su da ke karamar hukumar Itas-Gadau a jihar Bauchi.

Yace wacce ake zargin ta amsa laifin, an kuma same ta da wukar.

Tags