Amarya ta kone gidan mijinta a Adamawa
Amaryar ta shiga hannun ‘yan sanda a jihar.
Wata sabuwar amarya mai shekara 20 ta shiga hannu kan cinna wa gidan mijinta wuta a Jihar Adamawa.
An ruwaito cewar amaryar ta yi wannan aika-aika ne saboda rashin son angon nata.
- Jami’an MDD A Nigeria Sun Yi Jimamin Mutuwar Abokan Aikinsu A Gaza
- DAGA LARABA: Ƙalubalen Da Matan Aure Ma’aikata Ke Fuskanta
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa ita wannan amarya ta sanar da iyayenta cewa ba ta son yin auren kwanaki kadan kafin a daura.
Sai dai iyayen nata suka ce ba gudu ba ja da baya saboda sun riga sun raba katin gayyatar auren.
Bayan an daura auren ne ta sa wani mai tsubbu ya mata aiki ya sa mijin ya tsane ta har ta kai ga sakin ta.
Amma sai ta kasance maimakon mijin ya tsane ta, sai ita amarya ta bige da kara tsanar mijin nata.
Wasu rahotanni sun ce ita wanna amarya da mijin nata sun kulla wata yarjejeniya kafin daura aurensu.
Kakakin ’yan sandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce ruwaito ita amarya tana cewa “Mun shirya [da mijin nawa] cewa zai sake ni bayan auren.
“Bayana mun sadu da shi na roke shi ya sake ni, amma ya ki,” a cewarta.
Amaryar, wadda a halin yanzu take hannun ’yan sanda ta amsa laifin da ake tuhumar ta da aikatawa, kuma kwamishinan ’yan sandan jihar Adamawa, Afolabi Babatola, ya sanar cewa rundunarsa na kan bincikar lamarin.