Amarya ta mutu bayan sa’a 18 da aurenta

Wata amarya da ta yi fama da cutar dajin mama ta mutu sa’a 18 bayan da aka daura musu aure da angonta. Heather Mosher  ta kamu da cutar ciwon dajin mama tun a watan Disambar bara, an gnao cutar a ranar da saurayinta ya bukaci amincewarta don su yi aure. Dabe Mosher, saurayin Heather Mosher […]

Amarya ta mutu bayan sa’a 18 da aurenta

Wata amarya da ta yi fama da cutar dajin mama ta mutu sa’a 18 bayan da aka daura musu aure da angonta.

Heather Mosher  ta kamu da cutar ciwon dajin mama tun a watan Disambar bara, an gnao cutar a ranar da saurayinta ya bukaci amincewarta don su yi aure. Dabe Mosher, saurayin Heather Mosher ya gabatar da bukatarsa ne lokacin da yake kan keken dawaki.

Masoyan biyu sun hadu ne a wajen rawa a garin Hartford da Jihar Connecticut ta Amurka, har suka zama masoyan juna.

“Na gabatar da bukatata gareta ranar 23 ga Disambar 2016,” a cewar ango Dabe Mosher, kamar yadda ya fada wa tashar talabijin ta ABC. “Da safe sai muka tafi wajen likita bayan da ta ga wani kumburi a kan mamanta.”

Da aka gudanar da bincike kan kumburin nama, aikin da a turancin likita ake kira da “biopsy,” sai aka tabbatar Heather Mosher tana fama da cutar dajin mama, amma duk da haka Dabe Mosher bai karaya ba.

“fiye da komai, na yi matukar son nuna mata ba ita kadai ke fama da cutar ba,” inji shi.

“Idan kana tare da babban masoyinka. Cutar ta zamo tamkar tana kokarin sare kafadarka daga jikinka, ba zai yiwu haka ba. A manne kuke. Ita ce yarinyata,” a cewar Dabe Mosher.

Yayin da aka yi ta kone mata cutar ta hanyar sarrafa sinadarai bisa tsarin likitanci na “chemotheraphy,” sannan aka yi mata tiyata sau biyu, Heather da Dabe sai suka shirya bikin aurensu. Da a ranar 30 ga Disambar bara suka shirya , amma sai likitan ya ba su shawarar su yi auren da wuri,” a cewar angon.

Ango da amarya sun yi aurensu a cikin asibitin St. Francis Hospital da ke Hartford a Jihar Connecticut ranar 22, inda Heather Mosher ke kan gadon asibiti ana tarairarayar rayuwarta a hlin rai kwakwai, mutu kwakwai, duk da haka aka kakaba mata rigar amarya da sarkokin ado na mata.

Ango Dabe Mosher  ya fahimci cewa kalamanta na karshe da ta furta su ne amincewarta da zama matarsa. Ma’aikatan asibiti sune a jerin mahalarta  taron biki.