Amarya ta nemi saki bayan kwana 40 da aure

Da kyar take iya tsayawa kusa da mijin, ballantana ta haɗa jiki da shi. Sakamakon haka, bayan kwana 40 da yin aure, ta nemi a raba auren.

Amarya ta nemi saki bayan kwana 40 da aure

A kwanan ne wata mata ’yar kasar Indiya ta kai karar mijinta kwana 40 kacal da aurensu, inda ta yi ikirarin yana wanka sau ɗaya ko sau biyu a wata.

Matar da ba a bayyana sunanta ba daga Agra, a Jihar Uttar Pradesh ta Indiya, ta je cibiyar ba da shawara ga iyali don yin korafi game da rashin tsaftar mijinta, inda ta bayyana cewa ba kasafai mijin yake yin wanka ba, yana saka tufafi da dauɗa, kuma tana fama da warin bakinsa.

Ta kara da cewa, da kyar take iya tsayawa kusa da mijin, ballantana ta haɗa jiki da shi. Sakamakon haka, bayan kwana 40 da yin aure, ta nemi a raba auren.

Lokacin da cibiyar ba da shawara ta tambayi mijin, mai suna Rajash, ya yarda yana wanka sau ɗaya ko sau biyu a wata kuma yana tsaftace jikin ne ta hanyar yayyafa ruwa a jikinsa da Gangajal (ruwa mai tsarki daga kogin Ganges) sau ɗaya a mako.

Ɗaya daga cikin masu ba da shawara a cibiyar iyali da ke Agra ta shaida wa manema labarai cewa, sababbin ma’auratan sun fara samun sa-in-sa game da tsaftar mijin makonni kaɗan bayan ɗaurin aurensu.

Daga karshe, matar ta bar gidan, ta koma zama da danginta. Ba da daɗewa ba, danginta suka shigar da kara a ofishin ’yan sanda da ke yankin tare da neman a raba aurensu.

Matar ta ce, Rajash ya yi wanka sau 6 a cikin kwanaki 40 da suka gabata, wanda ya fi yadda ya saba yi, saboda ta dage. Jin labarin yanke shawarar rabuwa da shi, mijin ya yi alkawarin yin tsafta har ma da yin wanka a kullum, amma dangin matar sun ce ba ta son yin sulhu da shi.

A wani rahoto. wani ɗan kasar Taiwan ya taɓa sakin matarsa saboda tana wanka sau ɗaya a shekara, yayin da wani ɗan kasar Indiya kuma ya nemi a raba aurensu da matarsa saboda tana yin wanka sau ɗaya a cikin kwana goma.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC