Amarya ta nemi saki don mijinta na yi mata girki da wanke-wanke
Wata amarya Bamisiriya mai shekaru 28, mai suna Samar M. ta shiga damuwa saboda mijinta ya hanat a yin ayyukan gida, inda mako biyu da aurensu ta kai kara kotu tana neman saki, bisa dalilin cewa mijinta dan kasuwa ne mai shagon sayar da tufafi, amma shi yake yin komai na ayyukan gida. Samar ta […]
Wata amarya Bamisiriya mai shekaru 28, mai suna Samar M. ta shiga damuwa saboda mijinta ya hanat a yin ayyukan gida, inda mako biyu da aurensu ta kai kara kotu tana neman saki, bisa dalilin cewa mijinta dan kasuwa ne mai shagon sayar da tufafi, amma shi yake yin komai na ayyukan gida.
Samar ta ce mijinta mai shekara 31 ya hana ta gudanar da ayyukan gida, kuma tana cikin damuwa ganin cewa shi kadai yake yin komai, a cewar kafar sadarwa ta Al Arabiya. “Shi yake yin girki, ya share gida ya yi wanke-wanke da goge-goge.”
Matar wadda ba ta da wata sana’a da take yi, ta kai kara kotun sauraren kararrakin matsalolin iyali da ke sabuwar Alkahira, inda ta bayya cewa:”Mijina ba ya ba ni ’yancin kula da ayyukan gida, har ta kai ga ina jina tamkar bakuwar da aka sauke ta a otal.
“Shi ne ‘matar gidan’ shi ya sa na tsani rayuwata. Mun yi aure da mako biyu, amma shi yake girki da wanki, saboda ya nakalci yadda ake wanke kayayyaki masu launi. Sannnan ya goge su, ya yi shara, ya jera kayan abinci a firji (na’urar sanyaya abinci da abin sha).
“Yakan shirya girkinsa tun cikin dare don gudun kada ya bata lokaci a kansa washegari.”
Samar ta ce, takan kwashe lokutanta ne tana kallonsa a kowace rana, yayin da yake kai-kawo cikin farin ciki.
A mafi yawan lokuta wannan maigida yana zaune a gida saboda yana da dimbin ma’aikata a shagonsa.