Amarya ta nemi saki lokacin da suke hutun murnar aure

Wata amarya da ke hutun amarci tare da angonta a Hadaddiyar Daular Larabawa ta cike takardar neman saki a tsakaninta da angon a daidai lokacin da suke tsakiyar hutun murnar aurensu bayan da ta zargi angon cewa yana barinta da daukar nauyin biyan wasu al’amuran yau da kullum. Jaridar Albayan da ake wallafata cikin harshen […]

Amarya ta nemi saki lokacin da suke hutun murnar aure

Takardar saki

Wata amarya da ke hutun amarci tare da angonta a Hadaddiyar Daular Larabawa ta cike takardar neman saki a tsakaninta da angon a daidai lokacin da suke tsakiyar hutun murnar aurensu bayan da ta zargi angon cewa yana barinta da daukar nauyin biyan wasu al’amuran yau da kullum.

Jaridar Albayan da ake wallafata cikin harshen Larabci ta ruwaito; cewa matar da aka sakaya sunanta ta cike takardar shigar da kara gaban wata kotu da ke birnin Abu Dhabi inda take neman saki daga wajen angon nata wanda  dan kasar Iran ne. Amaryar da angon har zuwa rubuta wannan rahoto suna wajen shakatawar tasu wanda masu hannu da shuni ke ziyarta da zarar an daura aure.Matar dai tana ikirarin cewa angon nata wanda ta ba shi tazarar shekara 13 yana tambayarta ta biya kudin wutar lantarki da na ruwa  da kuma kayyayakin abinci da suke saye a manyan kantuna. Fusatacciyar amaryar ta ce za ta bi dukkan hanyoyin da suka dace don ta kwaci hakinta daga wajen angon nata domin ya sake ta.

Matar ta koka cewa mijin nata wanda ta kira shi da ‘mai son arha’ ko ‘A ci-bilis’, mijin ya umarce ta da ta yi rajistar dukkan kudaden harajin ruwa da na wutar lantarki da sunanta inda ya ce mata dukkan takardunsa sun bace bai gansu ba. Lauyan matar ya fada wa alkali cewa mijin ya umarci matar ta biya dukkan wasu kudaden al’amuran yau da kullum. Bai biya ko sisin kwabo ba a lokacin aurensu.

Matar ta kara da cewa, “Hatta kayan kujeru da gadaje ita ce ta saya da kudinta amma maimakon ya nuna gamsuwarsa wani lokaci sai ya rika nuna halin ko-in- kula da ita. Wannan ya sa ta shigar da shi kara kafin hutunsu na amarci ya kare.”