Amarya ta rasu yayin da sojoji ke artabu da Boko Haram a Borno

Mutane ukun sun rasu sakamakon harsasai da suka ƙwace suka same su yayin da suke gudu don tsira da rayukansu.

Amarya ta rasu yayin da sojoji ke artabu da Boko Haram a Borno

Wasu da ake zargin Boko Haram ne sun kai hari sansanin sojoji guda biyu a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno, inda mutum uku; ciki har da amarya suka rasu sakamakon musayar wuta da dakarun soji suka yi da maharan.

An ce maharan sun kai hari sansanin sojoji da ke Kofa da misalin ƙarfe 2:14 na dare, kafin daga baya suka kai hari wani wajen sojoji a Muna da misalin ƙarfe 2:30 na dare.

Shaidu sun ce maharan sun isa wuraren ne a kan babura suna harbe-harbe.

Duk da cewa sojoji sun samu nasarar fatattakar ’yan ta’addan, wasu mazauna yankin uku sun rasa rayukansu ne sakamakon harsasai da suka ƙwace suka same su.

Wata mazauniyar Kofa, Deborah Usman, ta ce wata sabuwar amarya da aka yi bikinta makonni uku da suka wuce tana cikin waɗanda suka mutu bayan harsashi ya same ta yayin da mutane ke gudu domin tsira rayukansu.

A yankin Muna kuma, mazauna garin sun ce mutane biyu sun rasu yayin da suke ƙoƙarin tsere wa harin, yayin da wata mata ta samu rauni sakamakon harsashin da ya same ta a gidanta.

Wannan hari ya faru ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan da wasu ’yan ta’adda suka kai hari wani sansanin soji da ke ƙauyen Logomani a Ƙaramar Hukumar Ngala a Jihar Borno, inda suka kashe soja ɗaya.

Da yake tabbatar da aukuwar harin, Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Operation Haɗin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce dakarun sun yi nasarar daƙile yunƙurin ’yan ta’addan na shiga Maiduguri da wasu sassan jihar.

Ya ce sojoji sun yi artabu da maharan a wurare daban-daban, lamarin da ya tilasta musu ja da baya.

Ya ce suna ci gaba da gudanar da aikin sintiri da bincike domin hana sake kai hare-hare.