Amarya ta yanke mazakutar angonta bayan wata hudu da aurensu

Angon yana kwance yana barci amaryarsa ta shigo ta hau kansa tana neman guntule masa mazakuta

Amarya ta yanke mazakutar angonta bayan wata hudu da aurensu

Wuka

Wani ango ya tsallake rijiya da baya, bayan da amaryarsa ta kusa raba shi da mazakutarsa ta hanyar zabga masa wuka.

Magidancin mai shekara 40 da haihuwa mai sana’ar noma da haya da babur yanzu haka yana kwance a gadon asibitin inda yake samun kulawan likitoci.

Angon ya shaida wa Aminiya lamarin ya farune a ranar 26 ga watan Mayu, 2024 bayan ya dawo daga Masallaci Sallar Asubahi inda ya dan kwanta kafin ya tashi zuwa neman abincinsa.

Sai kawai ya ji matarsa ta same shi yana barci ta haye jikinsa ta zabga masa wuka a mazakuta, kafin ya yi ihu aka kawo masa dauki.

Ya ce sun sami kimanin watanni hudu da yin aure kuma a halin da ake ciki tana dauke da cikinsa na wata biyu.

Acewarsa, auren soyayya da kaunar juna suka yi, kuma har ya zuwa lokacin da lamarin ya faru suna zaman lafiya shi da matarsa amma bai san dalilinta na aikata masa wannan aika-aika ba.

Ya kara da cewa a lokacin da matarsa ta yanka mazakutarsa ya nemi dauki daga jama’a, inda ya kwarma ihu, kuma su ne suka kwace shi.

Da farko an kai shi asibitin Kudan, ma’aikatan wurin suka ba da da shawara a wuce da shi zuwa Makarfi kafin suma suce a wuce zuwa Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya da ke Shika.

Ya ci gaba da cewa da zuwa tunda da dan sauranta bata gama guntulewa gaba daya ba wasu jijiyoyin ba su yanke duka ba, sai nan da nan likitoci suka shiga aiki kuma bisa dukkan alamu an yi nasara.

Koda wakilinmu ya tambaye shi ko idan ya warke zai iya dawowa da ita? sai yace yanzu lafiyarsa ke gabansa kuma ba ya tunanin zai iya ci gaba da zama da ita a matsayin matarsa.

Magidancin ya kara da cewa ai shi ko ya warke da wuya ya kara aure saboda riga  ya firgita da abin da ya faru da shi.

Mahaifiyar angon, wadda ita ke jinyar sa ta yi Karin bayani irin yadda suka zauna da surukar tata har zuwa faruwar lamarin.

“Duk da ba a gida daya muke zaune ba, Amman bai taba kawo mana koke a kanta ba, kuma a saninmu ba mu san ta da wani rashin lafiya ba, ko da irin shigar aljanu da ake cewa ba, suna zaune lafiya babu wani hatsaniya tsakaninsu,” in ji ta.

A halin da ake ciki iyayen matar sun nuna damuwa tare da kokarin biyan kudin magani amma iyayensa suka bukace su da su saurara har a gama da asibiti.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin likitocin da suka gudanar da tiyatar mazakutar, ko hukomomin asibitin, amma hakan ya ci tura saboda wai doka ba ta ba su damar fitar da sirin mara lafiya ba.

A halin yanzu dai amarya data yi wa angon nata wannan aika-aika tana hannun ’yan sanda suna gudanar da bincike.

Sai dai duk kokarin da wakilinmu ya yi domin hin ta bakin Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, abin ya ci tura duk da kiran wayarsa da rubutaccen sako da ya tora masa.