Amarya ta yi garkuwa da angonta a wajen bikin aurensa
Wata mata mai shekara 25 a Jihar Uttar Pradesh ta kasar Indiya ta yi garkuwa da ango lokacin da ya taka dan damalin bikin aurensa da wata yarinya. Bharti Yadab tare da haxin gwiwar wasu matasa da suka yi mata rakiya sun taimnaka mata a wajen wannan aika-aikar. A rahoton gidan talabijin NDTb, Bharti da […]
Wata mata mai shekara 25 a Jihar Uttar Pradesh ta kasar Indiya ta yi garkuwa da ango lokacin da ya taka dan damalin bikin aurensa da wata yarinya.
Bharti Yadab tare da haxin gwiwar wasu matasa da suka yi mata rakiya sun taimnaka mata a wajen wannan aika-aikar.
A rahoton gidan talabijin NDTb, Bharti da ango Ahsok Yadab sun daxe suna soyayya har ma sun yi auren sirrri. Sai daga bisani iyayen Ashok suka tursasa shi ya auri wata yarinyar.
Lamarin dai tamkar fim xin Indiya na Bollywood, Bharti ta shigo wajen bikin auren a motarta kirar SUb, rike da bindiga a hannu. “Wannan mutum yana sona; zai ci amanata idan ya auri wata daban . Ba zan bari hakan ta faru ba,” a cewarta lokacin da ta manna wa ango bakin bindiga a goshi.
An ruwaito cewa lamarin ya auku ne a garin Bundelkhand da ke Jihar Uttar Pradesh. Har yanzu ba a gano inda angon yake ba. Wannan lamarin ya shammaci bakin da suka halarci bikin, inda mamaki ya hana su cewa uffan.
“Akwai abin tuhuma ga xana. Domin duk sa’adda na kai masa ziyara a garin da yake aiki, ba zai kai ni gidansa ba, maimakon haka sai mu haxu a xakin ibadar hindu ya ciyar da ni a wajen sayar da abinci, sai ya tura ni gida,” a cewar mahaifin ango Ramhet Yadab, kamar yadda ya bayyana wa bakin da suka halarcin bikin.
Tuni dai iyayen amarya suka kai kara ga hukuma, inda suka yi rajistar laifin garkuwa da mutum. “Abin da ta aikata ya nuna cewa akwai matan da ke koya wa matasa hankali, kuma za a hukunta su saboda cin amana,” inji xan sandan a hirarsa da gidan talabijin na NDTb, wanda ke sha’awar majigin ‘Rebolber Rani.’