Amarya ta yi sanadiyyar mutuwar angonta da kanenta
Ana zargin wata sabuwar amarya mai suna Dausiya Abdulmumini, ’yar kimanin shekara 15 da kashe mijinta mai suna Saminu Usman, dan shekaru 27 tare da wani yaro dan uwanta mai suna Muhammadu Dasa dan kimanin shekara 8 da ke zaune tare da ita, ta hanyar cin abinci mai guba da ake zargin ita Dausiyar wadda […]

Ana zargin wata sabuwar amarya mai suna Dausiya Abdulmumini, ’yar kimanin shekara 15 da kashe mijinta mai suna Saminu Usman, dan shekaru 27 tare da wani yaro dan uwanta mai suna Muhammadu Dasa dan kimanin shekara 8 da ke zaune tare da ita, ta hanyar cin abinci mai guba da ake zargin ita Dausiyar wadda ba a dade da yi mata wannan aure ba ta zuba wa mijin.
Kazalika, akwai kanwar Saminu mai suna Shafa’atu, wadda ita ma ta ci sauran wannan abincin da aka zuba wa guba, kamar yadda Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Katsina D. B. Gwana ya shaida wa manema labarai a yayin gabatar da wadda ake zargin a gabansu. Ya ce bisa ga bayanan da suka samu, ita Dausiyya ta zuba gubar a abincin mijin nata ne, wanda ake zargin ko dama can ba ta sonsa.
Aminiya ta kalato cewa, lokacin da yake cin abincin ko bayan ya gama ya rage, sai shi wannan yaron wanda yake dan uwan matar ne da ita kuma kanwar mijin suka ci abincin. Ba a dauki wani dogon lokaci ba gubar ta fara aiki, sai amai. Nan da nan aka kai su asibitin Funtuwa, inda a can likita ya tabbatar da mutuwar Saminu mijin Dausiyya da kuma Muhammadu kanenta. Sai dai Shafa’atu ta tsira kuma har an sallamo ta daga asibitin.
Wannan al’amari ya faru a kauyen dan-Mayaki da ke cikin karamar Hukumar Bakori. Kamar yadda rundunar ’yan sandan ta tabbatar, Dausiyya ta amsa wannan zargi da ake yi mata a lokacin da ake yi mata tambayoyi.
A wani labarin kuma, rundunar ’yansandan ta ce ta kama wani mutun a kauyen Kuraye na karamar Hukumar Charanci mai suna Amadu Yahaya, wanda aka fi sani da Mai-kasuwa, dan shekara 45 bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekaru 5 fyade. An zarge shi da yin amfani da dakin injin nikan da yake da shi wajen yi wa yarinyar fyade.
Shi ma ya amsa wa jami’an cewa ya aikata wannan laifi. Sai dai Kwamishinan na ’yan sanda ya ce da zarar sun kammala bincikensu za su tura wadanda ake tuhumar zuwa kotu domin su fuskanci shari’a.