Ambaliya a Kano: An samu gawa mai shekara 21 ba ta lalace ba

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a Kano a ranakun Juma’a zuwa Lahadin da ta gabata ya jawo ambaliya a akalla kananan hukumomi 14 na jihar, inda ya zaizaye Makabartar ’Yankaba da ke birnin Kano.Wakilinmu da ya ziyarci makabartar ya tarar da ’yan aikin sa-kai suna gyaran kaburburan da suka rubza.Mai unguwar […]

Ambaliya a Kano: An samu gawa mai shekara 21 ba ta lalace ba

Gawar da aka same ta kalau bayan shekara 21 da binne ta.Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a Kano a ranakun Juma’a zuwa Lahadin da ta gabata ya jawo ambaliya a akalla kananan hukumomi 14 na jihar, inda ya zaizaye Makabartar ’Yankaba da ke birnin Kano.
Wakilinmu da ya ziyarci makabartar ya tarar da ’yan aikin sa-kai suna gyaran kaburburan da suka rubza.
Mai unguwar ’Yankaba, Alhaji Ya’u Badamasi da Aminiya ta tarar a wurin ya ce tun samar da makabartar shekara 27 da suka gabata, ba su taba samun ambaliyar da ta shiga ta yi barna haka ba.
Ya ce “Wani abin mamakin da muka gani shi ne yadda muka samu gawawwaki biyu da ba su lalace ba, alhali sun dade da binnewa,” Ya ce daya gawar ma an yi mata rauni a yayin hake ta, inda jini ya rika fita daga jikinta. Ya kiyasta cewa za ta kai kimanin shekara 21 da binnewa.
Ya ce “Ruwan ya karya katangar da ta kewaye makabartar ta yamma, inda ya share wasu kaburburan ya tafi da gawarwaki da dama. Akalla mun sake wa gawarwaki 38 sababbin kaburbura, amma wadanda ruwa ya tafi da su, sun fi wadanda muka binne yawa.”
Ya ce wadanda suka isa wurin da farko, sun ga abin mamaki da tashin hankali, inda gawarwaki da kasusuwan matattu suka rika yawo a kan ruwa. “Mutane da dama kuka suka rika yi saboda tausayi,” inji shi.
Mai unguwa Ya’u ya ce wani attajiri a yankin, Alhaji Ahmadu Dallatu ya bayar da Naira dubu 200, suka sayo bulo da siminti, don sake gina katangar, kuma ya ce mutanen da dama sun bayar da gudunmawar kasa da ta kai tifa 100 da aka yi amfani da ita wajen cike kaburburan da suka fada.
Ya ce, zai mika rahoton faruwar abin ga na gaba da shi, kuma ya ce tuni gwamnatin jihar ta yi alkawarin kai wa makabartar daukin gina magudanan ruwa da sake katange ta, kamar yadda ta yi irin wannan gyara a wasu makabartun jihar.
Shugaban kungiyar masu aikin makabartu ta Rahama, Malam Sani Jibirin ya shaidawa Aminiya cewa da farko sun fara amfani da ganyayyaki wajen toshe kaburburan, kafin daga baya wasu suka aike musu da agajin kayan aiki.
Ya ce ’yan kungiyar da sauran masu aikin sa-kai, sun shafe yini biyu suna gyara kaburburan, inda ya yi kira ga gwamnati ta kai musu dauki, domin aikin ya fi karfin jama’ar gari.
Daraktan Ayyuka na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Aminu Minjibir, ya ce ambaliya a jihar ta shafi mutum 1,489 kuma ta lalata gidaje 2,000. Ya ce sun aike da rahoto ga Hukumar a kasa NEMA, don daukar matakin da ya dace.