Ambaliya: An nemi mazauna yankin Kogunan Benuwe da Neja su yi ƙaura
Taswirar ta nuna muhimman yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa a faɗin Nijeriya, musamman a kusa da tashoshin da ke gaɓar kogin Benuwe da Neja.
Hukumar Albarkatun Ruwa ta Najeriya (NIHSA), ta yi gargaɗi al’ummomin da ke kusa da kogunan Benuwe da Neja cewa a akwai yiwuwar samun ambaliya ruwa cikin gaggawa, sakamon ƙaruwar ruwan saman da ake samu.
Darakta Janar na NIHSA, Umar Mohammed, a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, ya buƙaci mazauna kusa da bakin kogunan da su tashi, saboda ruwan kogin Benuwe ya kai matsayin da zai iya ambaliyar.
Ya ce rahoton hanyoyin ruwa iri. su: Lokoja, Umaisha, Makurdi, da Ibbi ya nuna a kodayaushe suna iya cika.
Mohammed ya yi gargaɗin, “Musamman yankin Makurdi, da aka tabbatar cikar kogin wanda ke da hatsarin gaske, tare da yankin Lokoja da sauran tashoshi kuma suna kusa da bakin kofa.”
Mohammed ya yi gargaɗin cewa hukumar kula da madatsun ruwa ta Kainji da Jebba na sa ido sosai tare da kula domin kare afkuwar ambaliyar ruwa a kogin Neja.