Ambaliya: Badaru ya bai wa Jigawa tallafin miliyan 20
Ministan ya yabawa gwamnatin jihar kan yadda ta ke bai wa waɗanda lamarin ya shafa tallafi.
Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya bai wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Jigawa, tallafin kuɗi Naira miliyan 20.
Ministan, wanda tsohon gwamnan jihar ne, ya bayar da kuɗin domin tallafa wa ayyukan agajin da gwamnatin jihar ke yi ga mutanen da Iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa.
- An kashe ’yan sanda 2 yayin arangama da ’yan shi’a a Abuja
- Tarihin Sarkin Ningi Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya
Hakan na kunshe ne, cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labaran ma’aikatar tsaro, Mista Henshaw Ogubike, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Badaru, ya bayar da tallafin ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga Gwamnan jihar, Umar Namadi, kan Iftila’in ambaliyar ruwa da ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi.
Badaru, ya kuma jajanta wa al’ummar jihar game da ambaliyar, wadda ta yi sanadiyyar lalata gonaki masu yawa a jihar.
Ya kuma jaddada ƙudurin Gwamnatin Tarayya na taimakawa jihar.
Badaru, ya yaba wa matakin gaggawa da gwamnatin jihar ta ɗauka kan lamarin da kuma waɗanda abin ya shafa.
“Aikin gaggawa da kuka yi na bayar da agaji ga waɗanda ambaliyar ta shafa abin yabawa ne,” in ji shi.
Jihar Jigawa dai ta fuskanci mummunar ambaliyar ruwa a daminar bana, lamarin da ya yi sanadin rasa rayuka da dukiya mai tarin yawa.